Daga USMAN KAROFI
Wata ƙungiyar masu satar bayanai da ake danganta da Iran ta samu damar shiga asusun imel na Daraktan FBI, Kash Patel, sannan ta wallafa hotuna na sirri da wasu bayanai a yanar gizo, rahoton kafofin watsa labarai na Amurka ya bayyana ranar Juma’a.
Ƙungiyar Handala Hack Team ta ce Patel “za ya ga sunansa a cikin jerin waɗanda aka samu nasarar satar bayanansu”.
Rahoton CNN ya bayyana cewa imel ɗin da aka sace sun haɗa da na sirri, harkokin kasuwanci da na tafiye-tafiye, wanda suka shafi shekaru 2011 zuwa 2022, kafin Patel a nada shi Daraktan FBI daga Shugaba Donald Trump.
FBI da Ma’aikatar Shari’a ba su mayar da martani nan da nan ba kan buƙatar sharhi.
Patel shi ne daraktan FBI na tara, kuma ya fara aiki a 2025. Sai dai shugabancinsa ya kasance cikin cece-kuce, inda masu sukar sa ke zargin sa da amfani da hukumar bin doka ta tarayya wajen tafiyar da harkokin tafiye-tafiye na kansa da kuma aiwatar da manufofin Shugaba Donald Trump.
Ƙungiyar da ta bayyana kanta a matsayin masu sa ido kan satar bayanai don goyon bayan Falasdinu, ta kuma ɗauki nauyin wani harin yanar gizo na baya-bayan nan kan kamfanin na’urorin kiwon lafiya Stryker.
Binciken da masana yammacin duniya suka yi ya nuna cewa ƙungiyar na da alaƙa da sashen leken asirin yanar gizo na Iran. Ta bayyana cewa harin na baya-bayan nan martani ne kan harin Amurka da Isra’ila a wani makarantar yara a Minab, kudu maso Iran, wanda ya hallaka fiye da mutane 170, mafi yawan su ‘yan mata ne makaranta.
Ƙungiyar ta ce wannan aiki ya nuna “farkon sabon babi a yaki na yanar gizo”. Iran ta yi barazanar ƙara kai hare-hare kan manyan sha’anin tattalin arzikin yammacin duniya a matsayin hanyar matsin lamba a rikicin Amurka da Isra’ila kan ƙasar.
