Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Gwamnan Jihar Anambra, Farfesa Chukwuma Soludo, ya amince da naɗin Misis Chiamaka Nnake a matsayin sabuwar Sakatariyar Gwamnatin Jiha (SSG), lamarin da ya sa ta zama mace ta farko da ta riƙe wannan muƙami a tarihin jihar.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Christian Aburime, ya fitar a ranar Litinin, ya ce naɗin ya fara aiki nan take, inda ta maye gurbin Farfesa Solo Chukwulobelu wanda ya fita daga muƙaminsa bayan rusa majalisar zartarwar jihar.
Nnake mai shekaru 39, ‘yar asalin Nawfia ce da ke ƙaramar hukumar Njikoka a jihar Anambra. Kafin wannan naɗin, ta taɓa riƙe muƙamin kwamishinar kasafi da tsare-tsaren tattalin arziki a jihar, inda ta taka muhimmiyar rawa wajen tsara da aiwatar da manufofin ci gaban tattalin arziki.
Haka kuma ta taɓa zama shugabar kamfanin Solution Fun City Limited, tare da riƙe wasu muhimman muƙamai a hukumomin jihar da suka haɗa da Hukumar Kula da Zuba Jari ta Jihar Anambra, Hukumar Haraji da kuma Hukumar Tallafawa ƙananan ‘Yan Kasuwa.
Sanarwar ta ce Nnake ta taka rawar gani wajen inganta harkokin kasuwanci da sauƙaƙa zuba jari a jihar, inda kuma take jagorantar shirye-shiryen tallafin jama’a da bunƙasa rayuwar al’umma.
Kafin shiga aikin gwamnati, ta yi aiki a matsayin babbar mai ba da shawara kan tsare-tsare a kamfanin PricewaterhouseCoopers (PwC), inda ta jagoranci ayyuka da dama a fannoni daban-daban, kuma ta samu lambar yabo ta CEO a shekarar 2021 saboda ƙwarewarta.
Nnake na da digiri na biyu (MBA) daga Lagos Business School, tare da kammala digiri na farko a fannin lissafin kuɗi da darajar farko daga Jami’ar Benson Idahosa. Ita mamba ce a ƙungiyar ƙwararrun masu lissafi ta duniya (ACCA), kuma tana ci gaba da karatun digirin digirgir a fannin manufofin jama’a.
Ta kuma halarci shirin koyon aiwatar da manufofin gwamnati a Harɓard Kennedy School, kuma tana daga cikin masu tsara dogon tsarin ci gaban jihar Anambra na ɓision 2070.
Nnake na da aure kuma tana da ‘ya’ya uku.
