Duk da saɓanin siyasa, NSA ya yi wa El-Rufai ta’aziyyar rasuwar mahaifiyarsa

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Mai bai wa Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Nuhu Ribadu, ya bayyana alhininsa kan rasuwar Hajiya Umma El-Rufai, mahaifiyar tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai.

Ribadu ya bayyana marigayiyar a matsayin uwa mai kulawa, inda ya ce yana da kyawawan abubuwan tunawa da suka haɗa shi da ita.

Ribadu ya bayyana hakan ne a cikin saƙon ta’aziyya da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Juma’a, inda ya jajanta wa iyalan El-Rufai tare da tuna lokutan da suka yi tare da marigayiyar.

“Inna lillahi wa inna ilayhi raji’un. Na yi matuƙar baƙin ciki da samun labarin rasuwar Hajiya Umma El-Rufai, uwar gidan iyalan El-Rufai. Ina da kyawawan abubuwan tunawa da muka yi tare, da kuma kulawarta irin ta uwa. A irin wannan lokaci, kalmomi ba sa iya bayyana girman rashin da aka yi.

Ina miƙa ta’aziyyata ga Malam Nasir El-Rufai da ɗaukacin iyalansa. Allah Ya gafarta mata, Ya sa ta huta a Aljannatul Firdaus, kuma Ya ba iyalan haƙurin jure wannan rashi,” in ji shi.

Tun da farko, News Point Nigeria ta rawaito cewa Hajiya Umma El-Rufai ta rasu ne a ranar Juma’a, inda wani ɗan uwa ya sanar da rasuwar ta cikin wani saƙo da ya wallafa a Facebook:

“Inna lillahi wa inna ilayhi raji’un. Daga Allah muka fito, kuma gare Shi za mu koma. Ina sanar da jama’a rasuwar kakata, Hajiya Umma El-Rufai, wadda ta rasu ‘yan awanni da suka gabata,” in ji saƙon.

Iyalan marigayiyar sun bayyana ta a matsayin uwa mai sadaukarwa, tare da yi mata addu’ar samun rahama da gafara.

Har zuwa lokacin da aka kammala wannan rahoto, ba a bayyana cikakkun bayanai kan musabbabin rasuwarta ba.

Wannan lamari na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da shari’o’i da suka shafi Malam Nasir El-Rufai, inda Gwamnatin Tarayya ta shigar da ƙara a gaban Kotun Tarayya da ke Abuja, kan zargin sa da yin katsalandan a harkokin sadarwa da suka shafi Ribadu a wani shirin talabijin.

By ukarofi