Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Wata cibiya da ke ƙasar Netherlands, wato Hague Institute for Innovation of Law (HiiL), ta ƙaddamar da wasu ƙa’idoji domin karewa da warware rikice-rikicen filaye tsakanin manoma da makiyaya a jihar Katsina.
Wannan ƙa’idoji na ƙarƙashin shirin Karfafa Zaman Lafiya Mai Ɗorewa (SPRING), wanda Ofishin Ci Gaban Ƙasashen Waje na ƙasar Birtaniya (UK) ya ɗauki nauyin aiwatarwa.
A lokacin ƙaddamar da ƙa’idojin, Kwamishinar Shari’a ta jihar Katsina, Justice Fadila Muhammadu Dikko, ta yi kira ga iyayen ƙasa, malaman addini, jami’an tsaro, manoma da makiyaya da su yi amfani da waɗannan ƙa’idoji domin tabbatar da ɗorewar zaman lafiya da ci gaban al’umma.
Kwamishinar, wadda Daraktan ma’aikatar, Aliyu Lawal Buhari, ya wakilta, ta buƙaci masu ruwa da tsaki da su yi aiki tuƙuru domin tabbatar da an aiwatar da ƙa’idojin yadda ya kamata, tare da ƙarfafa fahimtar juna, adalci da zaman lafiya a tsakanin al’umma.
Ta ƙara da cewa wannan shiri ya yi daidai da manufofin gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Raɗɗa, na samar da zaman lafiya, inda ta bayyana cewa gwamnan ya sanya hannu kan dokar da ta kafa cibiyoyin sasanta rikice-rikice a faɗin jihar.
Haka kuma, ta yaba da HiiL International bisa wannan shiri da suka kawo na ƙarfafa adalci da zaman lafiya.
Kwamishinar ta bayyana cewa fili na da matuƙar muhimmanci ga rayuwar manoma da makiyaya, amma sau da yawa yana zama tushen rikici a tsakaninsu.
A nata jawabin, jami’ar HiiL mai kula da sauye-sauyen shari’a a ƙasa (Justice Transformation Country Representative), Ijeoma Nwafor, ta ce waɗannan ƙa’idoji wani ɓangare ne na ƙoƙarin inganta samun damar adalci, wanda ya dace da muradun Majalisar Ɗinkin Duniya na tabbatar da adalci ga kowa.
Ta jaddada cewa an tsara ƙa’idojin ne tare da haɗin gwiwar masana, sarakunan gargajiya, shugabannin al’umma, jami’an tsaro, masana shari’a, manoma da makiyaya, da sauran masu ruwa da tsaki daga jihohin Katsina, Kaduna, Plateau da Benue.
Ijeoma ta kuma bayyana cewa baya ga rikicin filaye, sauran rikice-rikice kamar na ƙabilanci, addini da matsalar tsaro suna taka rawa wajen haddasa faɗace-faɗace a tsakanin al’umma.
Ta ce ƙaddamar da ƙa’idojin ya biyo bayan wani bincike da ya nuna cewa sama da mutane biliyan biyar a duniya ba su da damar samun adalci, yayin da a Nijeriya kimanin mutane miliyan 140 ke fama da irin wannan matsala.
A ƙarshe, Nwafor ta bayyana fatan cewa waɗannan ƙa’idoji za su taimaka wajen ƙarfafa haɗin kai da kyautata fahimtar juna a tsakanin al’umma.
Mahalarta taron sun haɗa da jami’an Ma’aikatar Shari’a ta jihar Katsina, ƙungiyar lauyoyi ta Najeriya reshen Katsina, ƙungiyoyin mata da sauran masu ruwa da tsaki
