INEC ta ƙara wa’adin mika rijistar mambobin jam’iyyun siyasa kafin zaɓen 2027

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta ƙara wa’adin mika rijistar mambobin jam’iyyun siyasa a matsayin shiri don zaɓen gama gari na 2027.

Matakin ya biyo bayan damuwa da jam’iyyun siyasa suka nuna a taron da hukumar ta gudanar ranar 24 Maris, 2026, kan wa’adin da aka tsara a baya, wanda ya kafa lokacin mika rijistar daga 1 zuwa 21 Afrilu, 2026.

A cikin wata sanarwa da Kwamishinan Ƙasa kuma Shugaban Kwamitin Bayar da Bayani da Ilimin Zaɓe, Mohammed Kudu Haruna, ya fitar, hukumar ta ce gyaran ya zama dole domin daidaita wa’adin da Dokar Zaɓe ta tanada.

“Hukumar ta amince ta daidaita lokacin mika rijistar mambobin jam’iyyun siyasa domin daidaita kwanaki 21 da Sashe na 77(4) na Dokar Zaɓe, 2026, da ranakun da jam’iyyun siyasa suka tsara da kansu,” in ji shi.

INEC ta kara jaddada cewa jam’iyyun siyasa suna da ‘yancin gudanar da zaɓukan farko na cikin gida a cikin lokacin da aka amince daga 23 Afrilu zuwa 30 Mayu, 2026, amma dole ne su bi dokokin mika rijista.

“Rijistar mambobin jam’iyya dole ne a mika ta kafin kwanaki 21 da gudanar da zaɓukan farko na jam’iyyar,” in ji sanarwar.

Sakamakon wannan gyara, sabon wa’adin ƙarshe na mika rijistar mambobin jam’iyyun siyasa shine 10 Mayu, 2026, maimakon ranar 21 Afrilu da aka tsara a baya.

Hukumar ta jaddada muhimmancin bin wa’adin, inda ta ce yin hakan yana da matuƙar tasiri wajen tabbatar da gudanar da zaɓe cikin tsari da gaskiya.

A halin yanzu, Najeriya tana da jam’iyyun siyasa 21 da aka yi rajista da su. Sun haɗa da:
Accord (A), Action Alliance (AA), Action Democratic Party (ADP), Action Peoples Party (APP), African Action Congress (AAC), African Democratic Congress (ADC), All Progressives Congress (APC), All Progressives Grand Alliance (APGA), Allied Peoples Movement (APM), Boot Party (BP), Labour Party (LP), National Rescue Movement (NRM), New Nigeria Peoples Party (NNPP), People’s Democratic Party (PDP), Peoples Redemption Party (PRP), Social Democratic Party (SDP), Young Progressives Party (YPP), Zenith Labour Party (ZLP), Youth Party (YP), da sabbin jam’iyyun Democratic Leadership Alliance (DLA) da Nigeria Democratic Congress (NDC).

By ukarofi