An gurfanar da ma’aikacin NYSC a kotu bisa zargin bai wa budurwa maganin zubar da ciki har ta mutu

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

An gurfanar da wani ma’aikacin Hukumar Yi wa ƙasa Hidima (NYSC), Abbas Olalekan, a gaban wata kotun majistare da ke Abeokuta a Jihar Ogun, bisa zargin haɗa baki da kuma ƙoƙarin zubar da ciki wanda ya yi sanadin mutuwar wata ‘yar bautar ƙasa mai suna ɓictoria Ariyo.

Olalekan mai shekaru 43, wanda ke zaune a yankin Oke-Ata a Abeokuta, ya fuskanci tuhume-tuhume na aikata laifi da suka haɗa da haɗa baki da kuma samar da magungunan zubar da ciki ba bisa ƙa’ida ba.

Mai gabatar da ƙara, Insfekta Lawrence Olu-Balogun, ya bayyana wa kotu cewa wanda ake tuhuma ya aikata laifin ne tsakanin watan Janairu zuwa Maris a yankin Laderin da ke cikin birnin Abeokuta.

A cewarsa, Olalekan ya haɗa baki da wasu da har yanzu ba a kama ba domin aikata laifin zubar da ciki, inda ya ba marigayiyar magungunan da ake zargin sun jawo mutuwarta.

An kuma bayyana cewa wanda ake tuhuma yana da alaƙa ta soyayya da marigayiyar wadda ke yi wa kasa hidima a karamar hukumar Abeokuta South, inda ake zarginsa da ɗaukar ciki ya kuma yi ƙoƙarin zubar da shi ta hanyar samar mata da magunguna.

Sai dai Olalekan ya musanta zargin da ake masa a gaban kotu.

Lauyan wanda ake ƙara, Bunmi Adelabu, ya nemi a ba shi beli bisa hujjar cewa dokar kasa ta ba kowane mutum damar a dauke shi ba mai laifi ba ne har sai an tabbatar da haka.

Alƙalin kotun, A.K. Araba, ta bayar da belin wanda ake kara kan kudi Naira 500,000 tare da sharaɗin samar da mutane biyu da za su tsaya masa, ciki har da dangi daya da kuma mutum mai aiki.

Ta kuma umarci cewa dole ne waɗanda za su tsaya masa su gabatar da takardun shaida da suka hada da rasitin wutar lantarki, hotunan fasfo guda shida, da kuma shaidar biyan haraji na shekarar 2026.

Daga nan kotun ta ba da umarnin a tsare shi a gidan gyaran hali na Ibara har sai ya cika sharudan belin, sannan ta dage shari’ar zuwa ranar 14 ga Afrilu, 2026 domin ci gaba da sauraron ƙarar.

By ukarofi