Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Rundunar Sojin Nijeriya ta cafke wani soja mai mukamin Staff Sergeant, Amoke Simon, bisa zargin aikata damfara ta kimanin Naira miliyan 114 da kuma yin ikirarin karya cewa ya taka rawa wajen kashe fitaccen shugaban masu garkuwa da mutane, Obioma Nwankwo wanda aka fi sani da “Osisikankwu.”
Majiyoyin soja sun bayyana cewa an kama wanda ake zargin ne a filin jirgin sama na Fatakwal yayin da yake ƙoƙarin tserewa zuwa Abuja, bayan binciken da ake yi kan zarge-zarge da dama da suka haɗa da damfara.
An ce haɗin gwiwar dakarun Brigade ta 14 da kuma ɓangaren kula da ladabtarwa na Diɓision ta 6 ne suka kama shi, bayan da bincike ya nuna cewa ya yaudari gwamnatin jihar Abia ta hanyar gabatar da kansa a matsayin ɗaya daga cikin waɗanda suka halarci aikin soja na shekarar 2010 da ya kai ga kashe Osisikankwu.
Rahotanni sun nuna cewa wannan iƙirari nasa ya sa aka ba shi kulawa da wasu alƙawuran tallafi, ciki har da taimakon lafiya.
Binciken farko ya kuma nuna cewa Hukumar EFCC ta daɗe tana bibiyar sa kan wasu zarge-zargen damfara, inda ake zarginsa da karɓar kusan Naira miliyan 100 daga wani kamfani, Naira miliyan 6 daga mutum ɗaya, da kuma damfarar wasu mutane da kusan Naira miliyan 8 kafin ya ɓuya.
Majiyoyi sun ƙara da cewa ya ƙara faɗaɗa ayyukansa na damfara ne bayan wani hatsarin babur da ya yi a Legas, wanda ya yi amfani da shi wajen neman tallafi daga mutane ta hanyar yaudara.
Sai dai bayanan rundunar soji da shaidun wadanda suka halarci aikin na shekarar 2010 sun karyata ikirarin nasa, inda suka tabbatar da cewa bai taba shiga wannan aiki ba, kuma ba shi da wata alaƙa da shi.
Wani babban jami’in soja da ya halarci aikin ya bayyana cewa rundunar da ta aiwatar da aikin karkashin jagorancin Brigadier Janar Timothy Oparon ce, inda aka tura sojoji 26 zuwa dazukan jihar Abia a watan Disambar 2010, suka kashe dan bindigar tare da kubutar da mutane kusan 10.
Haka kuma an karyata ikirarin sa na cewa ya samu rauni a wani aiki da ya shafi Boko Haram a jihar Borno, inda aka tabbatar da cewa bai taba shiga wani aiki a yankin Arewa maso Gabas ba.
Rundunar sojin ta bayyana ayyukan nasa a matsayin yaudara mai cutarwa ga mutuncin rundunar, tana mai jaddada cewa irin wannan hali na rage kima da sadaukarwar sojojin da ke fagen daga.
An kuma tabbatar da cewa ana shirin mayar da wanda ake zargin zuwa Lagos domin kammala bincike da kuma ɗaukar matakan ladabtarwa da suka dace a kansa.
