‘Yan sanda sun daƙile wani hari yayin yunƙurin kama shugaban ‘yan bindiga a Kano

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Jami’an rundunar ‘yan sandan Nijeriya a Jihar Kano sun yi nasarar daƙile wani hari da wasu fusatattun mutane suka kai musu yayin wani samame da suka kai domin kama wani da ake zargin shugaban ‘yan bindiga ne a karamar hukumar Bichi, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutum ɗaya tare da jikkata wasu da dama.

Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 6:30 na yammacin ranar 22 ga Maris, bayan samun kiran gaggawa daga ofishin ‘yan sanda na Tudun Wulli.

Aikin samamen wanda rundunar yaƙi da garkuwa da mutane ƙarƙashin jagorancin ASP Abubakar Musa ta jagoranta, ya biyo bayan sahihan bayanan sirri da suka nuna cewa wani da ake zargi shugaban ‘yan bindiga ne mai suna Muhammad, wanda aka fi sani da “Senator” ko “Kirchi,” yana cikin ƙauyen Tudun Wulli domin bikin Sallah.

Rahotanni sun ce an gan shi dauke da bindigar AK-47, amma ya tsere cikin jama’a yayin da jami’an suka yi yunƙurin kama shi.

Lamarin ya rikice ne bayan da wasu daga cikin mazauna yankin suka fara jifan jami’an da duwatsu da wasu abubuwa, inda hakan ya jikkata ASP Lawali Hamidu tare da lalata motar sintiri ta ‘yan sanda.

A yayin rikicin da ya biyo baya da kuma janyewar jami’an cikin dabara, mutane hudu sun samu raunukan harbin bindiga, inda aka garzaya da su asibiti domin samun kulawa.

Daya daga cikin wadanda suka jikkata, mai suna Halima Saidu, daga baya ta rasu, yayin da sauran ke ci gaba da samun sauki a asibiti.

An kuɓutar da jami’an ‘yan sanda cikin koshin lafiya, yayin da aka tura karin jami’an tsaro yankin domin tabbatar da doka da oda.

Rundunar ‘yan sandan ta tabbatar da cewa yanzu an shawo kan lamarin, tare da cewa ana ci gaba da bincike domin kamo wanda ake zargin ya tsere.

By ukarofi