02
Feb
Daga FATUHU MUSTAPHA Kasar China ta sanar da ɗaukar matakin haramta wa ɗalibai 'yan firame da na sakandare yin amfani da wayoyin salula a cikin aji. China ta ce, ta ɗauki wannan mataki ne domin kare ɗaliban daga fitinar intanet da kuma 'TV game' da kan hana ɗalibai maida hankali kan karatu yadda ya kamata. A wata takardar sanarwa da Ma'aikatar Ilimin ƙasar ta raba wa makarantu a Litinin da ta gabata, ma'aikatar ta ce daga yanzu ba a yarda ɗlibai a makarantun firamare da sakandare su riƙa amfani da wayoyi a aji ba. Tana mai cewa, "Duk ɗalibin da…
