Saudiyya: Zaki Yamani ya rasu

Daga FATUHU MUSTAPHA

Allah Ya yi wa fitaccen tsohon Ministan Harkokin Mai na Saudiyya, Ahmed Zaki Yamani, rasuwa. Yamani ya rasu ne a wata asibitin Landa a Litinin da ta gabata.

Wata ‘yar marigayin mai suna Mai Yamani, ta ce matsalar zuciya ce ta yi ajalin mahaifin nata, inda ya rasu yana da shekara 90.

Yamani na ɗaya daga cikin mutanen da ƙasar Larabawa ba za ta mancewa da su ba saboda irin rawar da ya taka wajen cigabanta.

A halin rayuwarsa, marigayin ya yi tsayin daka wajen bunƙasa harkokin mai na ƙasar Saudiyya.

A matsayinsa na ministan albarkatun mai na Saudiyya daga 1962 zuwa 1986, Yamani ya mamaye kasuwar mai ta Saudiyya har da ta duniya. Domin kuwa, kusan tsawon shekaru 25 ya kasance jigo mai ƙarfi a Ƙungiyar Ƙasashe Masu Haƙo Mai ta Duniya (OPEC) wanda duniya ta shaida tasirinsa.

An haifi Ahmed Zaki Yamani ne a 30 ga Yunin 1930 a birnin Makka. Ya yi karatu har zuwa matakin jami’a. Ya samu zuwa jami’ar Sarki Fuad I da ke Cairo a 1951, da Jami’ar New York a1955 da kuma Harvard Law School a 1956.