An sako direban Adamawa United da aka yi garkuwa da shi

Daga WAKILIN MU

An sako direban Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa na Adamawa United wanda aka yi garkuwa da shi a ranar Asabar da ta gabata.

An yi garkuwa da direban ƙungiyar ne a lokacin da suka faɗa hannun wasu ‘yan fashi da makami a kan hanyarsu ta zuwa birnin Legas don buga wasan da aka tsara musu a can.

Yazu haɗa wannan labari, babu wani cikakken bayani a kan ko sai da aka biya diyya kafin aka saki direban.

Tun farko, ‘yan fashin sun buƙaci a biya diyyar naira milyan N50 kafin su saki direban da suka yi garkuwa da shi, amma daga bisani sun rage farashin zuwa milyan ɗaya

Idan dai za iya tunawa, a ranar Asabar da ta gabata, ‘yan ƙwallon tare da jami’ansu suka shiga hannun ‘yan fashin a kan babbar hanyar Benin zuwa Ore yayin da suka yi nufin zuwa Legas domin buga wasan mako 11 tare da ƙungiyar Mountain of Fire and Miracles (MFM FC) da ke Legas ƙarƙashin shiryawar Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Nijeriya (NPFL).