Daga MOHAMMED U. GOMBE
Tun bayan aukuwar fashewar wasu abubuwa da aka samu a ƙasar Equatorial Guinea, hukumomin lafiyar ƙasar na ci gaba da yin kira ga jama’a da su bayar da gudunmawar jini da kuma buƙatar jama’a su shiga ayyukan sa-kai domin taimakawa wajen ceto rayuwar al’umma.
Aƙalla mutum 15 ne suka rasu sannan wasu ɗaruruwa sun jikkata sakamakon fashewar kamar yadda Ministan Lafiya na ƙasar ya bayyana.
Ibtila’in ya auku ne a Lahadin da ta gabata kusa da barikin sojoji a birnin Bata, inda aƙalla mutum 500 suka ji rauni.
Bayanai daga ƙasar sun nuna fashe-fashen sun auku ne sakamakon sakaci da aka nuna wajen ajiyar sinadarin ‘dynamite’ a barikin sojoji.
Hotunan faruwar fashewar sun nuna yadda ƙura da hayaƙi suka tarnaƙe sararin samaniyar inda lamarin ya auku da kuma ɓarnar da aka samu.
Haka nan, an ga wasu masu bada agaji na ta bincike a wurin domin gano waɗanda ke da sauran numfashi.
Shugaban Kasar, Teodoro Obiang Nguema, ya ce ƙarfin fashewar ya yi sanadiyar lalacewar gidaje da gine-gine masu yawa a yankin, tare da neman ɗauki daga ƙasashen duniya.
A saƙonni mabambanta da ta wallafa a shafinta na twita, ma’aikatar lafiyar ƙasar ta buƙaci ma’aikatan kiwon lafiya na sa-kai da su taimaka su kai agaji a asibitin da ke yankin Bata. Haka ma ta bukaci waɗanda ke da zarafin taimakawa da jini, su yi hakan.