Ranar Mata ta Duniya: Buhari ya taya murna ga matan Nijeriya

Daga AISHA ASAS

Fadar Shugaban Ƙasa ta yi taya murna ga matan Nijeriya da kewaye na bikin Ranar Mata ta Duniya na bana.

A wani bayani da fadar ta fitar a Lahadin da ta gabata, Shugaba Buhari ya ce bikin wannan shekara ya bada damar nuna karamci ga matan Nijeriya.

Ranar 8 ga Maris na kowace shekara, ita ce ranar da aka keɓe a matsasyin Ranar Mata ta Duniya inda akan yi biki tare da la’akari da irin nasarorin da mata suka samu a fannoni daban-daban na rayuwa.

Sanarwar da mai bai wa shugaban ƙasa shwara kan harkokin yaɗa labarai, Mr Femi Adesina ya fitar, Fadar Shugaban Kasar ta lissafo jerin sunayen wasu fitattun matan Nijeriya waɗanda suke aiki tare da Shugaba Buhari a gwamnatinsa.

Matan sun haɗa da: Ministar Kuɗi, Kasafi da Tsarin Ƙasa Zainab Ahmed, da Ministar Jinƙai, Agaji da Kyautata Rayuwa Sadiya Umar Farouq, da Ministar Harkokin Mata Pauline Tallen, da Ƙaramar Ministar Masana’antu da Zuba Jari Mariam Yalwaji Katagum, da kuma Ƙaramar Ministar Muhalli Sharon Ikeazor.

Sauran su ne; Ƙaramar Ministar Sufuri Gbemisola Saraki, Ƙaramar Ministar Abuja, Ramatu Tijjani Aliyu, Shugabr Ma’aikatan Tarayya, Folashade Yemi-Esan, Shugabar Hukumar NAFDAC, Mojisola Adeyeye, Mataimakiyar Shugaban Bababban Bakin Ƙasa (CBN), Aishah Ahmad, Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara ta Musamman, Mariam Uwais da dai sauransu.