’Yan wasan damben boksin da su ka fi samun kuxi a duniya

Daga UMAR M. GOMBE

Ɗaya daga cikin manyan wasannin da suka fi shahara a duniya shi ne, wasan damben zamani da ake kira a turance da Boxing. Kusan a iya cewa wannan wasa na cikin wasanni mafiya daɗewa a duniya, domin kuwa wasan dambe wasa ne da kusan ba wata al’umma da bata yi.

Masana sun gano cewa, akwai shaidu na tarihi da suka nuna shekaru 3000 kafin bayyanar Annabi Isa ana wannan wasa a tsohuwar Daular Misra. Amma wasan ya fara samun tagomashi ne a ƙarni na 7 tunda aka fara yin sa a wasan Olympic. Sai dai duk da haka sai a 1743 ne wani ɗan dambe mutumin Ƙasar Ingila da ake kira da, Jack Brownton ya fara sauyawa wasan tsari. Inda ya ƙirƙiro yin amfani da Akayau (Boxing glove), da kuma yin wasan ana hutawa zagaye-zagaye.

Koda yake a addinin Ƙasar girka sun bayyana cewa ababen bautar su ma na dambe, inda suka bayyana Apollo a matsayin ubangijin wasan dambe wanda hakan ke ishara da daɗewar sa a cikin su, amma dai shaidu sun tabbatar da cewa sai a 6 ga watan Janairu na 1681 ne aka fara shiga fage irin na zamani ayi dambe. A lokacin da wani hakimin Ingila mai suna, Christopher Monck a lokacin yana hakimin Albermarie kafin a naxa shi Gwamnan Jamaica ya haɗa wata gasar dambe, inda a wannan karawar ne aka gwabza tsakanin mahaucin sa da wani yaron gidan sa. Kuma ƙarshe dai mahaucin na sa ne ya yi nasara ya samu kyautar da shi hakimin ya saka.

Hausawa kan yi wa dambe kirari da “saga wasan mahaukata, mai hankali yana na daina, mahaukaci yana zan fara.” Duk irin haxarin da ke tattara da wasan na dambe, masana sun bayyana cewa ba shi ne wasa mafi haɗari a duniya ba, hasali ma baya cikin wasanni mafiya haɗari guda 10 a duniya, domin kuwa sun sanya shi ne a matsayin wasa na 11 acikin wasanni mafiya haɗari a duniya.

Tarihi ya tabbatar da ba a taɓa ɗan dambe da kowa ke shakkar shiga fage da shi ba irin Sony Liston, waɗanda suka ganewa idanun su abinda ke faruwa sun tabbatar da cewa, kusan dukkan wani xan dambe a wannan lokaci yana tsoron gamuwar su da Liston. Masu nazari sun tabbatar da cewa, ba a taɓa cin kofin ajin ƙwararru na damben boksin a zagaye na ɗaya ba har sau 7 sai akan sa. In banda Floyd Patterson ba a taɓa samun ɗan damben da ya haura zagaye uku da shi ba.

A tarihin damben sa ance sau 1 kawai ya taɓa faɗuwa. Amma kuma an haƙƙaƙe cewa bawani ɗan dambe da ya shahara duniya ta san da shi kuma take jinjinawa bajintar sa ba kamar Mohammed Ali. Haka kuma an tabbatar da cewa damben nan da ake wa laqabi da “thriller in Manilla” wanda aka gwabza tsakanin Buster Douglas da Mike Tyson a shekarar 1990, shi ne wasan dambe mafi shahara a tarihin duniya.

To amma ba kawai ana dambe ne kawai saboda sha’awa ko nishaɗi ba, ana damben zamani ne a matsayin sana’a. ‘Yan dambe na samun maƙudan kuɗaɗe a saboda wannan sana’a ta su. Kusan a iya cewa, suna cikin ‘yan wasa suna cikin waxanda suka fi karvar kuɗi a duniya. A wannan nazari namu mun zaƙulo muku ‘yan dambe da suka shahara kuma a dalilin sana’ar tasu suka tara abin duniya.

Mike Tyson – $ 30 million

Tyson baya bukatar gabatawar ga mai karatu, domin a ‘yan shekarun baya kusan sai da ya shiga bakin duniya, a saboda tuhumar da aka yi masa na yunƙurin yi wa wata mata fyaɗe a wani otel. A wasanni 58 da ya taɓa bugawa a rayuwar sa, ya samu nasara a wasanni 50 wannan ne ma ya sa ake masa kirari da “mutum mafi illa a duniya” saboda yadda ya ringa wuju-wuju ina Gabas da ‘yan dambe.

Joe Calzaghe – $21 Million

Ɗan shakara 48, Calzaghe mutumin Qasar Wales ne, saboda qwarewar sa a damben ajin matsakaita ya sanya ake masa kirari da “abin tinƙahon Wales”. Ya shahara a wasan dambe tsakanin 1993 har zuwa 2008. Ya nuna gwanancewar sa a wasan dambe na ajin matsakaita. Inda ya lashe kambuna da dama ciki kuwa har da na WBO, wanda kuma shi ne ya fi kowa daɗewa ɗauke da wannan kambu domin sai da ya ɗauke shi sau 21 ya kuma shafe shekara 10 yana riqe da kambun. A yanzu dai haka ya aje damben ya shiga harkar fim gadan-gadan.

Naseem Hamed – $33 million

Hamed ɗan ƙasar Biritaniya na cikin ‘yan dambe da tarihi zai jima bai mance da su ba. Shi ne ɗan damben da bai yaɓa kare fuskar sa a yayin da yake damben ba, hakan ya sanya ya zama ya fita daban a cikin ‘yan dambe. Ya yi dambe har sau 37 a ajin matsakaita, kuma sau xaya kawai aka tava kai shi ƙasa har zuwa lokacin da ya yi ritaya yana ɗan shekara 28.

Muhammad Ali – $50 million

An haifi zakaran damben duniya a ran 17 Janairu, 1942. Ya fara dambe tun yana ɗan shekara 12, amma damben nasa ya fara fitowa ne a lokacin da ya cika shekara 18. Ya fara ɗaukar kambun sa na farko ne a shekarar 1960. Muhammad Ali ya zama mafi shaharar xan dambe a tarihin duniya. A shekarar 1984 bayan ya kai mazaje da dama qasa, aka gano yana da cutar nan ta rawar jiki wato Parkinson, dan haka ya ajiye dambe ya koma taimakon mutane gajiyayyu. A shekarar 2005 aka bashi lambar yabo mafi girma a Ƙasar Amurka. Ya rasu a ran uku ga watan Yuni na shekarar 2016.

George Foreman – $300 million

An haifi George Foreman a shekarar 1949, ya fara damben tun yana matashi. Tauraruwar Foreman ta fara haskawa tun lokacin da ya yi nasarar doke abokin karawar sa da ba a taɓa doke shi ba, Joe Frazier tun daga wannan lokaci ne ya zama zakaran gwajin dafi acikin ‘yan dambe. Ya buga dambe daga 1969 zuwa 1977 daga nan ya yi ritaya saboda kasa samun dammar sabunta kwantarigin sat un bayan da Muhammadu Ali ya yi masa bugun kuf-ɗaya. Sai dai ya sake dawowa dambe a shekarar 1985 ya kuma cigaba da fafatawa da abokan adawa har zuwa 1987.