An ceto baƙin haure 483 a gaɓar tekun Libya, inji IOM

Daga UMAR M. GOMBE

Hukumar Kula da Sha’anin ‘Yan Gudun Hijira ta Ƙasa da Ƙasa ta Majalisar Ɗinkin Duniya (IOM), ta ce baƙin haure 483 aka ceto daga gaɓar tekun Libya a yammacin ƙasar.

Hukumar ta ce dogarawan tsaron tekun Libya sun yi aikin ceton baƙin ne a lokuta daban-daban.

IOM na mai cewa duk da dai an bai wa baƙin taimakon gaggawa da sauran kulawar da ta dace, sai dai ta ce tashar ruwan Libya ba ta da tsaro.

Ta ci gaba da cewa baƙin haure sama da 4,500 ne aka daƙile ko aka cece su a wannan shekara wanda a ƙarshe aka tsare su.

A baya-bayan nan, Ƙasar Libya ta zama maƙetarar ɗaruruwan baƙin haure masu burin ƙetarewa zuwa ƙasashen Turai don neman arziki, wanda sukan zaɓi bi ta Libya ne don kauce wa mataka tsaro.