Duk littafin da na rubuta ba ƙagaggen labari ba ne ya faru da gaske – Fatima Ibrahim Garba Ɗanborno

*Zaluncin ‘yan kasuwa ne ya durƙusar da marubutan mu – Fatima

DAGA AISHA ASAS

Fatima Garba Ɗanborno ba za a kira ta ɓoyayya ba musamman a wajen ma’abota karance-karancen littafan Hausa, domin ta yi fice wajen fitar da littattafai masu tarin faɗakarwa gami da ilimintarwa da kuma nuni cikin nishaɗi. Shi ya sa a wannan makon Jaridar Manhaja ta zagaya don zaƙulo wa masu karatu ita don jin wace ce ita? Me ya kai ta ga fara rubutu da shiga harkokin marubuta tsundum? Tare kuma da jin irin nasarori da faɗi-tashin da ta yi kafin ta zama cikakkiyar marubuciya? Duk waɗannan za ku ji a cikin wannan tattaunawar:

Za su so ki gabatar mana da kan ki.
Suna na Fatima Ibrahim Garba Ɗanborno, wacce duniyar rubutu suka fi sani da (Teemah Zaria). Ni ‘yar asalin Maiduguri ce a ƙaramar hukumar Biu. Nan ne asalin mahaifina. Sai dai mun tsinci kanmu a Zaria ne a dalilin aiki na mahaifina. Na yi makarantar firamare har zuwa gaba da sakandire a birnin na Zaria.

Ya aka yi ki ka samu kanki a duniyar rubutu?
Dalilai da dama suka sanya na tsinci kaina a duniyar rubutu da marubuta. Amma babban dalilin ba zai wuce ni ma ina da sha’awar miƙa saƙo domin ya tafi kaitsaye wuraren da nake fata. Uwa-uba sha’awar abun, da kuma dama can Allah ya rubuta muna da abinci a cikinsa.

Wace irin rawa marubuci ke takawa a rayuwar al’umma?
Marubuci madubi ne da ke haska rayuwar al’umma. Idan marubuci ya ga dama zai iya haskowa al’ummarsa halin da ƙasarsa take ciki, da tarin matsaloli birjik da ke cikin ƙasarsa, a cikin salonsa na jan hankali, zai sake haska wa al’umma hanyoyin da ya kamata su bi domin ganin sun samu mafita. Shi marubuci bai taɓa yin rubutu ba tare da mafita ba, duk girman matsaloli kuwa.

Wace shekara ki ka fara rubutu?
Na fara rubutu 2007, sai kuma a 2009 ne rubutun ya yi ƙarfi sosai. Ban samu damar fitarwa ba sai 2013.

Zuwa yanzu kin yi littattafai nawa?
Na yi littattafai kamar haka: ‘Kowa ya kwana lafiya’, da ‘Zuciya’, da ‘Sirri’, da ‘Mafarin lamarin’, da ‘Ina muka dosa?, ‘A Mafarkin Sa’, da ‘A Karan Kaina’, da ‘Rubutacciya’, sai kuma ‘Akwai Lokaci’. A taƙaice dai na rubuta littattafai guda tara kenan, na goman insha Allahu yana tafe kwanan nan.

Me ya sa rubutun mata ya fi na maza karɓuwa?
Saboda mata sun fi maza sanin sirrin mata ‘yan’uwansu, don haka sun fi maza sanin salon da ya kamata su yi amfani da shi wajen jawo hankulan al’umma. Musamman yadda duk yawancin rubutun a kan matsalolin cikin gida ake yi. Duk da haka akwai mazan da idan suka yi rubutu za ki rantse mata suka yi. Wasun su kuma abinda ke kashe su a rubutu maimaita magana wanda shi ke saurin gundurar mai karatu.

Me ya durƙusar da kasuwar littattafan adabin kasuwar Kano?
Abubuwa da yawa sun taru sun durƙusar da kasuwar littattafai; a ciki akwai cin zalin marubuta da wasu daga cikin ‘yan kasuwa su ke yi. Kasuwa tana tafiya ne muddin aka san haƙƙin mutum kuma ake kyautata masa. Kasuwar adabi ba ta mutu ba, marubutan ne suka ja baya saboda jikinsu ya yi sanyi, sun so ƙwarai a taimaka masu wajen gyara sana’arsu, sai aka samu wasu mutane masu son zuciya waɗanda burinsu su durƙusar da marubutan.

A taki fahimtar me ya janyo yawaitar rubutun batsa?
Rubutun batsa kala-kala ne, akwai wanda wasu marubutanmu suke yi da daɗewa, amma ba wai suna nuna komai ƙarara ba ne, a’a suna bayyana wasu abubuwa ne wanda furta su yake da girma a wurinmu. A wancan lokacin babu wanda ya ɗauki hakan a matsayin rubutun batsa da zai tashi hankulan jama’a. Wanda da irin su ake yi a yanzu ba na jin akwai wanda zai ɗaga kai ya furta wata magana. Marubuta sun yi ƙoƙari wajen tsaftace rubutunsu. A wancan lokacin masu irin rubutun da nake gaya maki ɗin ba su da yawa. Amma a yanzu an dawo da rubutun batsa! Ina nufin na yanzu shi ne asalin rubutun batsan.

Akwai rubuce-rubuce da aka turo min in duba a online wanda ya firgita ni, a hakan kuma akwai yara waɗanda ba su wuce shekaru 20 zuwa ƙasa da suke karanta irin labaran nan ba. Akwai marubutan ‘online’ da na sani masu tsaftace rubutunsu, waɗanda suka sa min sha’awar yin rubutu a ‘online’ don ada ba na yi. Amma da na haɗu da manyan nan sai da na girgiza.

Kina ganin da a ce ba a karantawa yaushe za a rubuta? Mu marubuta muna yin rubutu ne don a karanta, idan ba a karanta ba aka bar mana kayanmu gobe za mu yi?
Kullum sai dai a fito ana cewa marubutan online sun yi batsa, a maimakon a haɗa kai a ƙi karantawa sai ki ga har kuɗi ake biya ana siya ana karantawa. Don haka ba komai ke jawo yawaitar rubutun batsa ba, sai yadda mutane suka nuna sun fi son irin rubutun, idan ba irin sa ba ba za su karanta ba.

Ta yaya za a iya hana rubutun da ke ɓata tarbiyya?
Babu hanyar hanawa, sai dai hanyoyin da za a rage, sai kuma ke uwa ki sanya idanu akan ‘ya’yanki. Ba wai don yarinya ta girma ki ce kin sakar mata komai ba. Yanzu yanar gizo ta zama abin tsoro. A nan ne ake yin rubutun da zai iya taɓa tarbiyyar yara. A can baya na sha cewa ƙarya ce babu rubutun da ke ɓata tarbiyya kasancewar ni makaranciya ce. Ina karanta littattafan su Anti Fauza, da su Anti Beli da sauran su. Ban taɓa cin karo da rubutun da zai ɓata tarbiyya ba, sai ma rubutun da zai sa idan ka na aikata ba daidai ba ka ji tsoro ka daina.
Amma yanzu a wayar hannu za ki karanta rubutun da babu marabarsa da kallon tsiraici.
Don haka sai an daina karantawa an bar su da abinsu sannan za su ga babu riba su daina. Sai marubutanmu na gaske sun dage da jawo waɗancan a jiki suna nuna masu kuskurensu sannan za a samu a rage. Don ni kaina na ci nasara a kan wata har shawarata ta yi amfani ta daina irin rubutun.

Da gaske rashin tallafi da marubuta ba sa samu daga gwamnati ne ya durƙusar da su?
Idan akwai rashin tallafi a cikin durƙusar da marubuta sai dai hakan ya zo daga baya. Amma abin da ya fara durƙusar da marubuta ‘yan kasuwa ne. Idan ma marubuta muna da buƙatar tallafi ba zai wuce na yadda za mu dinga siyar da littattfanmu ba.

Wane lokaci ki ka fi sha’awar yin rubutu?
Na fi sha’awar yin rubutu a lokacin damina, idan ana ruwan sama ko kuma lokacin sanyi. Sannan basira tana zuwar min ne a lokacin da nake cikin ɓacin rai. Idan na yi rubutu cikin ɓacin rai rubutun ya fi ban sha’awa da ma’ana. Ba na son matsowa kusa da ‘Laptop’ a lokacin da nake cikin tsananin farin ciki.

Kin taɓa samun karramawa a fagen rubutu?
An karrama ni zai kai sau shida. Na samu karramawa na ‘Best writer’ har sau biyu.

Daga lokacin da ki ka fara rubutu zuwa yanzu kin samu wasu nasarori da rubutun ya zama sila?
Alhamdu lillah! Babu abin da zan ce da rubutu sai hamdala. Mutanena su ne nasarata. A da can baya ba na son shiga mutane, ba na sakin jiki in yi hira da kowa sai ‘yan’uwana. Amma dalilin rubutu na zama ta jama’a. Don haka mu mun gode Allah. Rubutu ya yi mana riga da wando.

Ƙalubale fa?
Wai! Babu abin cigaba da za ki yi wanda babu ƙalubale. Idan ina tuna wasu daga cikin kalubalen da na samu wataran na kan yi murmushi kawai don ya riga ya faru, wataran kuma na kan ji hawaye ya cika idanuna, a cikin hawayen sai in yi hamdala in kara gode wa Allah don komai ya zama tarihi. Amma babban kalubalen da na kasa mance shi ba zai wuce yadda na sha wahala kafin aka amince har na fara rubutu ba. Domin da farko ma gani ake yi shirme kawai nake son yi. To da yake ina da wani hali, idan na furta ina son yin abu to fa sai na yi ɗin, duk wuya duk sauƙi. Idan na ce ina son mallakar abu, duk yadda zan yi muddin ba zan kauce hanya ba sai na samu abun nan. Hakan ce ta kasance a lokacin da nake ƙoƙarin ganin na zama marubuciya. Duk yadda ake yaga takardun da na rubuta hakan ba ya hana ni sake rubuta wani. Gaskiya wannan kalubalen ya kasa bace min, musamman yadda a yanzu yayan nawa ya fi kowa alfahari da ni.

Shin ana iya koyon rubutu?
Eh ana iya koyo, amma idan dama can mai koyon ya kasance yana da baiwar rubutun. Domin dai kullum faɗi muke yi rubutu baiwa ce. Sau tari masu koyon ba su san suna da irin wannan baiwar ba, amma sai su ga kome aka koya masu suna ɗauka. Ni kaina na koyar da rubutu a cikin aji, na koyar da rubutu a online. Masu baiwar rubutun sun iya har sun zama marubuta, waɗanda ba su da baiwar abun, sun gaza a hanya.

Mene ne burinki a fagen rubutu nan gaba?
Burikana suna da yawa. Amma yanzu babban burina kasuwar littafi da ke ƙoƙarin mutuwa ta dawo. Don har yanzu kasuwar ba ta mutu ba, amma idan har masu ƙokarin fitarwan suka ja baya, babu ko shakka kasuwar za ta mutu.

Shin rubutu sana’a ce?
Rubutu sana’a ce, duk da masu sha’awar rubutun sun fi yawa a cikinmu, amma duk abin da za ka sa kuɗi ka yi aikin sa, sannan ka samu riba ko da ta biyar ce, babu ko shakka sana’a ce.

Labarin littafin ‘Rubutacciya’ ya faru da gaske?
Gaskiya dukkan labaraina da nake rubutawa sun faru da gaske, sai dai kwaskwarima irin na marubuci. Sau tari basirar rubutun ba ta zuwa min sai na ga wani abu da ya faru, sai ya jawo hankali na in ɗora alkalamina. Don haka labarin ‘Rubutacciya’ ya jima a cikin kwanyata ina juya yadda zan rubuta shi kafin daga baya Allah ya ba ni ikon rubutawa.

Waɗanne ababe ne idan marubuci ya cika yin su a rubutu su ke gundurar mai karatu?
Wato yawaita maimaita magana, ko kuma marubuci ya tsaya a wuri ɗaya ya yi ta bayani ratata. Shi mai karatu ado da kwalliyar labari ya fi komai ɗaukar hankalinsa. Shi labari ba a sakin sa kara zube. Abin da ya ke kashe marubuta da yawa kenan, domin za ki ga suna da labarai masu kyau, amma ba su san yadda za su ƙulla zaren labarin ba. Sai ki ji ana cewa wance ba ta iya labari ba, bayan ba labarin ne ba ta iya ba, a’a yadda za ta kulla zaren labarin na ta ne ba ta sani ba.

Wani lokaci za ki ga marubuci ya yi shimfiɗa mai kyau a labarinsa, amma sai alƙalamin ya kuɓuce a hannunsa a tsakiyar labarin, hakan zai sa duk ƙoƙarinsa a farko ya tashi a banza. Shin me ke kawo hakan?
Akwai abin da ake kira ‘Block’ a rubutu, wanda kowane marubuci yana samun sa a cikin ƙwakwalwarsa. A duk lokacin da marubuci ya dage yana rubutu yana cin karo da ‘Blocking’. Wato komai ya kulle. Idan marubuci ya cika matsawa kansa shi ne ake samun shirmen rubutu ko a tsakiya ko a ƙarshe. Idan kuwa kina son kauce wa wannan, ya zama dole idan ki ka tsinci kan ki a irin yanayin ki ajiye alƙalaminki ki ci gaba da wasu sabgoginki, har zuwa lokacin da ƙwaƙwalwarki za ta warware ta dawo daidai.

Duk da cewa ba kya cikin marubuta na baya sosai, amma sunanki ya yi tambari, yayin da littattafanki suka zama abin son makaranta. Ko za mu iya sanin sirrin ɗaukakar ki?
Har yanzu a cikin marubuta ni ƙarama ce, ina nan ina rarrafe ban kai ga miƙewa ba, bare in fara tafiya. Duk da hakan littattafaina sun samu karɓuwa ne a dalilin bincike. Marubuta da yawa suna raina bincike, ko kuma in ce a can baya ƙirƙirar komai ake yi a cikin littafi har ma da garuruwa da unguwanni. Amma yanzu an samu ci gaba, duk inda marubuci zai ambata a cikin littafinsa akwai shi a zahiri. Don haka nake jawo hankalin sabbin marubuta da ma wasu tsofaffin da kafin su ɗora alƙalaminsu a kan rubutu su fara yin bincike. Bincike yana taimako ƙwarai da gaske.

Kina rubutun Fim?
Yanzu mafi yawan marubutanmu sun koma rubutun fim, saboda duk marubucin da ya iya rubutun littafi babu ko shakka zai iya yin na fim. Don haka ni marubuciyar fim ce.

Za mu iya sanin wasu daga cikin fina-finan da ki ka rubuta?
Na rubuta ‘Sirri’, da ‘Shamakin Rayuwa’, da ‘Aljannar Mace’. Akwai guda uku da na rubuta an ce ana aikin su sai dai ban san sunan da suka sanya masu ba, kasancewar sunan da na sa sun ce za su canza. An yi ‘shooting’ ɗin su, sai dai ba a sake su ba sakamakon lalacewar kasuwa.

Daga ƙarshe wace shawara za ki ba wa marubuta ‘yan’uwanki?
Shawarar ba za ta wuce in roƙe su Allah da Annabi ka da su bar mana kasuwa babu komai babu kowa ba. Shawarata ka da wasu su kashe mana guiwa har ya zamana an daina karatun littattafai a kasuwa. Ina jin takaici matuƙa idan na tuna manyan marubuta sun ja baya. Don Allah mu daure mu ci gaba da fitar da littattafai ko don ci gaba da raya adabinmu.

Mu na godiya ƙwarai.
Ni ke da godiya.