03
Mar
Daga AISHA ASAS Ƙasar Iran ta ce ba yanzu ne lokacin da ya dace a yi magana kan batun makaman nukiliya ba duba da halin da ƙasashen Amurka da Turai suka nuna. Iran ta ƙi amincewa da ta yi zaman tattaunawa da ƙashashen Amurka da Turai domin tattauna yadda za a farfaɗo da yarjejeniyar nukilya ta 2015, tana mai cewa dole sai Amurka ta ɗage duka takunkuman da ta ƙaƙaba mata kafin ta amince. A cewar mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Iran, Saeed Khatibzadeh, la'akari da halin da Amurka da wasu ƙasashen Turai suka nuna, ya sa Iran…
