Za su farmake mu cikin mako guda, inji Trump bayan gano ƙarfin makaman Iran ya wuce yadda yake tunani

Spread the love

Shugaba Donald Trump na Amurka ya ce Iran tana da makamai masu linzami sama da yadda ake tunani da fari, wanda hakan ya sa take shirin kai wa Amurka hari.

Trump ya bayyana haka ne a ranar Litinin yayin jawabi ga ‘yan majalisa na jam’iyyarsa ta Republican a taron shekara-shekara na nazarin tsare-tsaren da aka yi a Florida.

A cewarsa, ƙasar za ta iya kai musu hari cikin mako ɗaya duba da shirin da suka yi wa yaƙin.

Hakan na zuwa ne jim-kaɗan bayan jawabin Shugaban na Amurka cewa hare-haren soji da take kai wa Iran ka iya ƙarewa nan ba da jimawa ba.

A wata hira wayar tarho da gidan jaridar CBS, Trump ya bayyana cewa dakarun tsaron Amurka sun yi wa ƙarfin sojin Iran lahani.

A cewar rundunar sojin Amurka, sama da wurare 3,000 na ƙasar Iran aka kai wa hari a makon farko na yaƙin.

A ranar Lahadi ne Iran ta naɗa Ayatollah Mojtaba Khamenei a matsayin sabon jagoran addinin ƙasar bayan halaka mahaifinsa am makon farko na yaƙin.

By ukarofi