Mu ne za mu yanke hukuncin lokacin da yaƙin zai ƙare – Martanin Iran kan kalaman Trump na yaƙinsu ya kusa ƙarewa

Spread the love

Rundunar juyin juya halin ƙasar Iran ta yi watsi da kalaman Shugaba Donald Trump na cewa yaƙin da Amurka da Isra’ila suka ƙaddamar akan Iran ya kusa ƙarewa, yayin mayar da martani akan furucin shugaban Amurkan.

Trump ya bayyana a wani taro a Florida cewa Amurka ta samu gagarumar nasara a yaƙin, kuma akwai yiwuwar kawo ƙarshensa nan kusa.

Shugaban Amurka ya ce Iran na shirin kai hari kan Amurka kuma tana ƙoƙarin farfado da shirinta na Nukiliya.

A kan yiwuwar kai hari kan sabon jagoran addinin Iran, Ayatollah Mojtaba Khamenei, Trump ya ce ba abu ne da ya kamata a furta ba, kodayake ya bayyana rashin jin daɗinsa kan zabin.

A cikin martanin da rundunar IRGC ta yi, ta ce “Za mu cigaba da gwagwarmaya har zuwa ƙarshe… har sai Amurkawa sun bar wannan yankin.”

Wannan na zuwa ne yayin da Trump ya buƙaci Iran ta “miƙa wuya ba tare da sharaɗi ba a yaƙin da Amurka da Isra’ila ke yi da ƙasar.

By ukarofi