Daga AISHA ASAS
A can kwanakin bayan a shafin Iyali mun taɓa darasi kan yadda rarabuwar kawuna a addini ya jefa Musulunci cikin halin da yake a yanzu. Inda a halin da muke ciki kowane ɓangare na kallon ɗaya a matsayin wanda ba muslmi ba.
Wannan na ɗaya daga cikin dalilan da ya rage ƙarfin Musulunci duk da tarin mabiya da yake da shi.
Shafin ƙasashen Waje na wannan makon zai tattauna kan yaƙin Iran da yadda ƙasashen Musulunci suka koma gefe suna kallo yayin da wasu ke ganin hakan a matsayin daidai.
Tun bayan juyin juya halin Musulunci na shekarar 1979 a Iran, ƙasar ta kasance cikin taƙaddama da ƙasashen yamma, musamman Amurka da Isra’ila, saidai a duk tsayin shekarun abinda ke tsakanin su bai kai kwatankwacin abinda ke gudana a yanzu ba. Kasancewar a can baya faɗan ya fi kama da na siyasa, saɓanin yanzu da aka fara kece reni a tsakanin ƙasashe biyu da suka dunƙule wuri guda don yaƙar ƙasa ɗaya, wato Amurka da Isra’ila zuwa ga Iran.
Yaƙin ya samu sanadi ne na zargin da ake yi na ƙasar Iran ta ƙarrfafa shirin mallakar makamin ƙare dangi wato nukiliya tare da zargin ta da tallafa wa wasu “ƙungiyoyin yaƙi” a yankin gabas ta tsakiya.
Da wannan ne ƙasar Amurka da Isra’ila suka fake wurin gina laifukan da suka sa ta tsaurara takunkumai ga ƙasar, hakan bai yi mata ba, ana tsaka da yiwar samun maslaha a tsakanin ƙasashen ta hanyar tattauna, Amurka ta kai farmaki wanda ya yi sanadiyyar rayukan Iranawa masu matuƙar muhimmanci ciki kuwa har da jagoran ƙasar Ayatollah Ali Khamenei.
Kafin mu yi zurfi kan bayyana yaƙin da irin alƙiblar da ya dosa, bari mu karkata zuwa ga tambayar da ta fi ɗaukar hankali ta shin ina ƙasashen Musulunci suka tsaya a wannan rikici?
Kamar yadda Mohamad Safa, Jami’in Diflomasiyya na Majalisar ɗinkin Duniya ya faɗa cewa, wannan faɗan fa ba na Iran ba ne, na Musulunci ne, da ya kamata a ce dukkan musulmai sun hankalta.
Lokaci ne da ya kamata musulman duniya su haɗa kai su yaƙi abinda zai iya zama barazana gare su a gaba, su ajiye bambance-bambancen da ke tsakaninsu na addini, su yi riƙo da Musuluncin kawai.
Ya kuma ƙara da cewa, “Ni ba cikakken mai goyon bayan tsarin mulkin Iran ba ne. Ina da saɓani da su a abubuwa da dama, kuma ni ba ɗan Iran ba ne. Ni musulmi ne, kuma a wurina yanzu ba abinda ya dame ni na ko ni sunni ne ko shia.
Yanzu ya bayyana sarai ba sa ƙoƙarin ɓoye gaskiya, Shugaba Donald Trump da Sanata Lindsey Graham sun bayyana cewa wannan yaƙi ne da Musulunci, kuma Benjamin Netanyahu ya ce sun haɗa kai ne don yaƙi da Musulmi Shia da Sunni gaba ɗaya.
A yau sun kashe jagoran addinin Musulunci na Shia, gobe kuma za su iya kashe wani jagoran addini na Musulunci na Sunni.
Ko dai mu haɗu a matsayin musulmi a ƙarƙashin dokar ƙasa da ƙasa domin tunkarar ta’addancin su, ko kuma za su ci gaba da kashe mu ɗaya bayan ɗaya, indan har muka ci gaba da kasancewa a cikin rarrabuwa da rauni irin haka,” inji Mohamad Safa.
Duk da cewa Iran na ɗaya daga cikin ɗariƙu masu tsauri, kuma an zarge ta da aikata ababen da dama na cutar da wani ɓanagre na musulmai don kawai ba su bi ɓangaren ta ba, haka Shia tana ɗauke da ababe da dama da suke da ayar tambaya kan sahinancin musuluncinsu. Kuma ba za mu kawar da kai ba kan yiwar wata rana ta yaƙi wasu ɓangarori na musulmai ba, saidai hakan ba yana nufin kawar da kai ga gaskiya ba.
Wannan lamari na yaƙin Iran tamkar yara ne da suka fito ciki ɗaya, sai ya kasance kowane ya zaɓi hanyar da yake ganin ta fi masa na daga halayya, hakan kuwa ya janyo matsala tsakaninsu, inda wani ɓangaren ke ƙoƙarin lurar da ɗaya hanyar da ya bi ba daidai ba ce, wannan dalilin ya kai su ga faɗa.
Yayin da suke cikin wannan taƙaddamar, sai aka samu wasu can suka ɗaura aniyyar yaƙar wannan ahalin, wanda su a wurinsu ba ruwansu da ɓangarori da rashin fahimtar da ke tsakaninsu, abinda suka sa gaba kawai son su kawar da wannan ahali daga doron ƙasa, ko su rage masa ƙarfi ta hanyar sanya masu tsoro, da kashe duk wani da suke ganin zai iya kawo masu matsala ko bayyana aƙidu na gidan.
Ga mizani ta hankali, abinda ya kamata wannan ahalin su yi shi ne, su ajiye wannan saɓanin nasu a gefe, ba wai sai sun bar shi a zuciya ba, su dunƙule wuri ɗaya, su ɗabaƙa azancin zancen nan da ya ce, abinda ya taɓa gira, shi ne zai taɓa ido. Su yaƙi wannan barazana da ta shafe su duka, idan sun yi nasara, sai su dawo su cigaba da faɗan cikin gida wanda suka tabbatar wa duniya na su ne su kaɗai.
Mu yi duba da yadda ƙasashe irin su Burtaniya, Faransa da ‘yan uwanta suka nuna goyon bayan su ga Amurka, duk da ‘yar tsamar da ke tsakanin wasunsu da ƙasar Amurka tun bayan hawan Trump mulki. Hakan bai sa suka zuba ido suna kallon faɗan ba don kawai suna da saɓani da ƙasar ba, dalili kuwa suna kallon ƙasar Iran a matsayin ƙasar Musulunci wa
nda shi Musuluncin barazana ce gare su baki ɗaya, don haka faɗan nasu ne duka.
A ranar 28 ga watan Fabrailu, 2026, ƙasashen Amurka da Isra’ila suka ƙaddamar farmakin soji mafi girma a kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran tun bayan juyin juya hali na shekarar 1979.
Bayan kai harin na farko, aka samu tabbacin mutuwar Jagoran addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei, duk da cewa daga farko ƙasar ta musanta, saidai daga baya ta tabbatar da hakan tare da mutuwar wasu jiga-jigan tsaron ƙasar.
Wannan ya sa ƙasar ta fara ramuwar gayya wadda har ake mamakin irin ta, duba da cewa ko kusa ƙasashe da dama ba su yi tsammanin ƙasar ta Iran ta mallaki irin makaman da take kai farkami da su ba. Hakan kuwa ya ba ta damar rama kaso mai yawa na daga cikin farmakin da aka kai mata duk da iƙirarin Amurka da ƙawayenta na cewa suna da na’urorin kaɓo jiragen yaƙin Iran don haka ba zata iya cutar da su ba.
Saidai a mizani na hankali, ko yanzu aka kai ƙarshen wannan yaƙi za mu iya cewa Iran ta yi nasara, domin ƙasa biyu ta yaƙa a lokaci ɗaya, wanda su kuma ƙasashen biyu nasarorin da suka samu raba daidai za a yi.
Saidai tambayar da ta fi ci wa musulmai rai ita ce, shin yaushe ne musulman duniya za su haɗa kai su ajiye bambance-bambancen aƙida su tunkare barazanar da ta dunfaro Musulunci?
