Kasashen Waje

Erdogan zai gana da Putin kan samar da hatsi a duniya

Erdogan zai gana da Putin kan samar da hatsi a duniya

Shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan na shirin ziyartar Rasha domin tattaunawa da takwaransa na ƙasar, Vladimir Putin game da farfaɗo da yarjejeniyar fitar da hatsi daga tekun Black Sea. Ana sa ran tattaunawar tsakanin Erdogan da Putin ta yi armashi ta yadda za a iya amfani da ita wajen faɗaɗa yarjejeniyar zaman lafiyar Ukraine. Jam’iyyar Erdogan mai mulki ta shaida wa manema labarai cewa, za a gudanar da wannan tattaunawar ce a wurin shaƙatawa da ke gavar Tekun Black Sea a birnin Sochi, inda za su mayar da hankali kan kawar da matsalar ƙarancin abinci da ke tunkarowa. Watakila shugaba…
Read More
Ɗumamar yanayi za ta fara laƙume rayuka a duniya – IMF

Ɗumamar yanayi za ta fara laƙume rayuka a duniya – IMF

Asusun Bada Lamuni na Duniya IMF ya yi gargaɗin cewa, matsalar ɗumamar yanayi na barazana ga matalautan ƙasashe, wanda idan har ba a ɗauki matakan gaggawa ba, za ta fara haifar da hasarar rayuka nan da shekarar 2060. IMF ya ce, za a samu ƙaruwar kaso 8.5 na adadin rayukan da za a yi asara, musamman a yankunan da ke fama da matsalar sauyin yanayi, kuma kaso 14 na waɗannan ƙasashe za su fuskanci qaruwar tsananin zafi. Daga cikin ƙasashe 39, wanɗanda ke ɗauke da kusan mutane biliyan guda na al’ummar duniya, rabi daga cikinsu da ke fama da wannan…
Read More
Juyin mulki: Sojoji sun naɗa Kanal Brice Nguema a matsayin sabon shugaban Ƙasar Gabon

Juyin mulki: Sojoji sun naɗa Kanal Brice Nguema a matsayin sabon shugaban Ƙasar Gabon

Sojojin da suka yi juyin mulki a ƙasar Gabon sun sanar cewa Kanal Brice Clotaire Oligui Nguema ne sabon shugaban ƙasar wanda hakan ya kawo ƙarshen mulki na shekara 55 da zuri'ar Bongo suka shafe suna yi a ƙasar. Manhaja ta rawaito a ranar Laraba sojojin ƙasar suka hamɓarar da Ali Bongo Ondimba daga karagar mulki tare da soke zaɓen da aka ce Odimba ne ya lashe. Sun ce zaɓen da ya gudana a ƙasar cike yake da maguɗi. A ranar Talata da daddare Hukumar Zaɓe ta ƙasa ta bada sanarwar sakamakon zaɓen inda Ali Bongo ya samu ƙuri'u kashi…
Read More
Sojoji sun karɓe mulki a Gabon

Sojoji sun karɓe mulki a Gabon

Sojojin ƙasar Gabon sun sanar da ƙwace iko daga gwamnati mai ci tare da rushe sakamakon zaɓen da aka bayyana Ali Bongo Ondimba a matsayin wanda ya lashe. Kafin sanarwar sojojin, bayanai sun ce an shafe tsawon sa’o’i ana jin ƙarar harbin bindiga a sassan Libreville babban birnin ƙasar kodayake babu tabbacin ko musayar wuta ce ko kuma kawai sojojin na harbin iska ne. Cikin jawabin kai tsayen da suka yi ta gidan talabijin ɗin ƙasar da safiyar Laraba, sojojin sun sanar da rushe dukkanin sassan gwamnati ciki har da majalisun dokoki da kuma kotun kundin tsarin mulki. A cewar…
Read More
Shugaban Ƙasar Zimbabwe ya nemi yin tazarce

Shugaban Ƙasar Zimbabwe ya nemi yin tazarce

Shugaban Ƙasar Zimbabwe mai shekaru 80, Emmerson Mnangagwa, ya nuna ra'ayinsa na sake maimara wasu shekaru a kujerar shugabancin ƙasar. Shugaba wanda ya kasance shugaban Ƙasar Zimbabwe na biyu tun bayan dogon mulkin shugaba Robert Mugabe da ya shafe shekaru kusan 40 a mulki. Emmerson Mnangagwa, shi ne tsohon mataimakin shugaban ƙasa Mugabe, ya karɓi ragamar shugabancin ƙasar bayan juyin mulkin, ya kuma yi alƙawarin bunƙasa tattalin arziki ƙasar, da bayar da 'yancin faɗin albarkacin baki, da sassauta takurawar da ake yi wa 'yan adawar da ke magantuwa kan wa'adin mulkin Mugabe, da kuma taɓarɓarewar dangantaka da ƙasashen yammacin duniya.…
Read More
Ƙungiyar AU ta dakatar da Jamhuriyar Nijar daga dukkan sha’aninsu

Ƙungiyar AU ta dakatar da Jamhuriyar Nijar daga dukkan sha’aninsu

Ƙungiyar Tarayyar Afrika, AU, ta fitar da Nijar daga cikinta, tare da umurtar sojojin da suka yi juyin mulki su koma barikinsu don yin abin da aka san su da shi, wato tsare ƙasa. Ƙungiyar ta bayyana hakan ne a wata takarda da ta fitar a ranar Talatar da ta gabata, sannan ta ƙara kira da babbar murya ga sojojin da su saki hamɓararen shugaban ƙasar Mohamed Bazoum. Bayan wannan, ƙungiyar ta AU ta ɗau alwashin sake bibiyar irin matakan da ƙungiyar ECOWAS ta ɗauka kan Jamhuriyar Nijar don ganin ta inda ya kamata ta qara kutsa kai da nufin…
Read More
Juyin Mulkin Nijar: Sai bayan shekara uku za mu miƙa mulki ga farar hula – Tchiani

Juyin Mulkin Nijar: Sai bayan shekara uku za mu miƙa mulki ga farar hula – Tchiani

Daga BASHIR ISAH Jagoran juyin mulki a Jamhuriyar Nijar, Abdourahamane Tchiani, ya bayyana cewa sai bayan shekara uku sojoji za su miƙa mulki ga farar hula a ƙasar. Ya bayyana hakan ne a jawabin kai-tsaye da ya yi wa 'yan ƙasar a talabijin ranar Asabar da daddare. Jawabin nasa na zuwa ne bayan tattaunawar da suka yi da tawagar ECOWAS ƙarƙashin jagorancin tsohon Shugaban Ƙasar Nijeriya, Janar Abdulsalami Abubakar (mai ritaya). Janar Tchiani ya ce a tsakanin wata ɗaya mulkin sojin zai kafa kwamitin da zai samar da sabon kundin tsarin mulkin ƙasar. Ya ƙara da cewa, duk da dai…
Read More
Sojojin juyin mulki a Nijar sun naɗa ministoci duk da gargaɗin ECOWAS

Sojojin juyin mulki a Nijar sun naɗa ministoci duk da gargaɗin ECOWAS

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Masu juyin mulkin jamhuriyar Nijar sun kafa sabuwar gwamnati duk da umarnin Ƙungiyar Ƙaya Tattalin Arzikin Ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS). Shugabannin sojojin sun sanar da sabbin ministoci 21 a wata doka da aka karanta a gidan talabijin na ƙasar. Wannan dai na zuwa ne gabanin wani taron gaggawa da shugabannin ƙungiyar ECOWAS ta Yammacin Afirka suka yi kan juyin mulkin da aka yi a Nijar, bayan da hafsoshin sojin ƙasar suka bijirewa wa'adin da aka ba su na dawo da zavavven shugaban ƙasar. Janar Abdourahamane Tchiani ne ya sanar da sabuwar gwamnatin Nijar, wanda…
Read More
AU ta mara wa ECOWAS baya game da ƙudurorinta kan juyin mulkin Nijar

AU ta mara wa ECOWAS baya game da ƙudurorinta kan juyin mulkin Nijar

Daga BASHIR ISAH Ƙungiyar Ƙasashen Afirka (AU) ƙarƙashin jagorancin Moussa Faki Mahamat, ta ce tana goyon bayan matakan da ECOWAS ta ɗauka kan Jamhuriyar Nijar ɗari bisa ɗari. AU ta bayyana goyon bayan nata ne ga ƙoƙarin da ECOWAS ke yi wajen maido da mulkin dimokuraɗiyya a ƙasar Nijar wadda a yanzu take hannun sojojin juyin mulki. Faki Mahamat ya nuna damuwarsa dangane da rashin kulawar da hamɓararren shugaban Nijar, Mohamed Bazoum ke fuskanta a hannun sojojin da ke riƙe da shi. Cikin sanarwar bayan taron da AU ta fitar mai ɗauke da kwanan wata 10 ga Agusta, shugaban ƙungiyar…
Read More