Erdogan zai gana da Putin kan samar da hatsi a duniya

Shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan na shirin ziyartar Rasha domin tattaunawa da takwaransa na ƙasar, Vladimir Putin game da farfaɗo da yarjejeniyar fitar da hatsi daga tekun Black Sea.

Ana sa ran tattaunawar tsakanin Erdogan da Putin ta yi armashi ta yadda za a iya amfani da ita wajen faɗaɗa yarjejeniyar zaman lafiyar Ukraine.

Jam’iyyar Erdogan mai mulki ta shaida wa manema labarai cewa, za a gudanar da wannan tattaunawar ce a wurin shaƙatawa da ke gavar Tekun Black Sea a birnin Sochi, inda za su mayar da hankali kan kawar da matsalar ƙarancin abinci da ke tunkarowa.

Watakila shugaba Erdogan ya yi wannan ganawar da Putin a ranar 8 ga watan gobe na Satumba, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Bloomberg ya rawaito duk da cewa, ita gwamnatin Turkiyya ba ta sanar da ainihin ranar da za a yi zaman ba tsakanin shugabannin biyu.

Ita ma fadar Kremlin ta shugaba Putin ta tabbatar da ganawar da za a gudanar da ita kowane lokaci daga yanzu, amma ba ta faɗi ranar da za a yi ba.

Shugaba Erdogan ya yi amfani da zumuncin da ke tsakaninsa da Rasha da Ukraine a yunƙurinsa na haɗa ƙasashen biyu kan teburi guda na sulhu.

Rasha da Ukraine na kan gava wajen fitar da hatsi ga qasashen duniya kuma yarjejniyarsu ta farko ta taimaka ƙwarai wajen rage farashin kayan abinci da suka yi tashin goron zabi a duniya.