AU ta mara wa ECOWAS baya game da ƙudurorinta kan juyin mulkin Nijar

Daga BASHIR ISAH

Ƙungiyar Ƙasashen Afirka (AU) ƙarƙashin jagorancin Moussa Faki Mahamat, ta ce tana goyon bayan matakan da ECOWAS ta ɗauka kan Jamhuriyar Nijar ɗari bisa ɗari.

AU ta bayyana goyon bayan nata ne ga ƙoƙarin da ECOWAS ke yi wajen maido da mulkin dimokuraɗiyya a ƙasar Nijar wadda a yanzu take hannun sojojin juyin mulki.

Faki Mahamat ya nuna damuwarsa dangane da rashin kulawar da hamɓararren shugaban Nijar, Mohamed Bazoum ke fuskanta a hannun sojojin da ke riƙe da shi.

Cikin sanarwar bayan taron da AU ta fitar mai ɗauke da kwanan wata 10 ga Agusta, shugaban ƙungiyar ya yi kira ga sosjojin da suka yi juyin mulkin da su hanzarta hana ci gaban lalacewar dangantakar da ke tsakanin Nijar da ECOWAS.

AU ta ce ba za su lamunci tsare shugaban ƙasar da aka zaɓe shi ta halastacciyar hanya ba.

Daga nan, shugaban na AU ya yi kira da a gaggauta sakin Shugaba Bazoum da sauran ahalinsa da ake tsare da su ba bisa ƙa’ida ba.