Ƙungiyar AU ta dakatar da Jamhuriyar Nijar daga dukkan sha’aninsu

Ƙungiyar Tarayyar Afrika, AU, ta fitar da Nijar daga cikinta, tare da umurtar sojojin da suka yi juyin mulki su koma barikinsu don yin abin da aka san su da shi, wato tsare ƙasa.

Ƙungiyar ta bayyana hakan ne a wata takarda da ta fitar a ranar Talatar da ta gabata, sannan ta ƙara kira da babbar murya ga sojojin da su saki hamɓararen shugaban ƙasar Mohamed Bazoum.

Bayan wannan, ƙungiyar ta AU ta ɗau alwashin sake bibiyar irin matakan da ƙungiyar ECOWAS ta ɗauka kan Jamhuriyar Nijar don ganin ta inda ya kamata ta qara kutsa kai da nufin ƙara matsa lamba ga sojojin da suka yi juyin mulkin.

Kawo yanzu Ƙungiyar ECOWAS ba ta sauya matsayarta ba kan yiwar ɗaukar matakin soja kan Jamhuriyar Nijar, a ƙoƙarinta na ganin sun tilastawa sojojin mayar da mulkin a inda suka karɓe shi. Inda suka tabbatar da a shirye suke don aika sojoji a Nijar matuqar matakan silhu ba su yi tasiri ba.