Lalata da ɗalibai a jami’o’in Nijeriya

Ga duk mai bibiyar al’amuran da suka shafi shafin yanar gizo, ko kuma in ce harkar yaɗa labarai a qasar nan ya san yadda a ’yan watannin nan ake yawan samun koke-koken game da yadda wani Malaman Jami’o’i ke lalata da ɗalibansu don su ba da maki, ko kuma don a kai su inda ba su kai ba a harkar jarabawa.

Ko ba a ce komai ba, wannan wani mummunan abu ne da za a iya cewa bai kama da hakali ba, ko kuma mu ce wani abu ne da ya zama bala’in wanda idan ba a yi hankali ba zai iya zama wata annoba da za ta taɓa tarbiyyar ’ya’yanmu da kuma kawo mummunan nakasu a harkar ilimi a ƙasar nan.

Irin wannan abu da waɗannan vata-garin Malamai suke yi, wani abu ne da aka jima ana yinsa, sai dai bai zama ruwan dare ba kamar a ’yan watannin nan, inda ake kamawa, tare da ɗaukar mataki a wasu makarantu. Amma wasu kam har yanzu suna nan suna cin karensu babu babbaka.

A wani bincike da Ƙungiyar Bankin Duniya ta gudanar a shekarar 2019, kashi 70 cikin 100 na matan da suka kammala karatu a jami’o’in Nijeriya na fuskantar cin zarafi ta hanyar lalata da su kuma adadin na ƙaruwa duk shekara.

A bara, a wani taron yaƙi da cin hanci da rashawa da aka yi a Abuja, tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya ce cin zarafin mata ya kai wani mataki mai ban tsoro a jami’o’in qasar nan, tare da “jima’i don maki” kuma yana cikin ayyukan cin hanci da rashawa da hukumomi ke bincike.

Ya ce, gwamnatinsa ta damu, kuma hukumar da ke yaqi da cin hanci da rashawa (ICPC) tana tuhumar cin zarafin mata a matsayin cin zarafi a cibiyoyin ilimi.

Ko da yake bai bayar da wata ƙididdiga ba, Buhari ya ce ɗalibai sun fito da yare don bayyana nau’ukan cin hanci da rashawa a jami’o’i.

Sai dai duk da haka za a iya cewa ana samun sauƙi, domin an saba idan irin waɗannan abubuwa suna faruwa ba a ɗaukar wani mataki a kai, bilhasali ma idan wata ɗaliba ta kuskura ta kai ƙarar irin wannan cin zarafi, to kashinta ya bushe, domin Malaman za su haɗe ma ta kai ne, su gaba-gaba har wajen Hukumar makarantar su ƙaryata ta, a ƙarshe a ce ita ce ba ta da gaskiya.

To amma a ’yan watannin nan abin ya zama ba haka ba, domin duk yarinyar da ta kai irin wannan ƙara, to Hukumar makarantar tana ɗaukar matakin da ya dace wajen hukunta irin waɗannan miyagun malaman.

Akwai musalai da dama inda aka ɗauki irin wannan mataki. Misali, a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, an kama wani Malami wanda ya yi fice a irin wannan aika-aikar, inda kuma bayan bincike ta hanyar wani ƙaƙƙarfan kwamiti, aka sallame shi.

Haka zalika, a Jami’ar Tarayya da ke garin Dutsin-ma ta Jihar Katsina nan ma ana yawan samun irin waxanda matsalolin, domin akwai wata ɗalibar da ke cewa, wasu daga ciki Malaman jami’ar, kusan kashi saba’in bisa ɗari, suna neman ɗalibansu, idan kuma ɗaliban suka ƙi ba su haɗin kai, sai su riƙe su a jarrabawa.

Haka kuma a jihar Ekiti, Hukumar gudanarwar Jami’ar jihar ta kori wani Malamin Jami’ar mai suna Olola Aduwo, korar kuma irin korar da Marigayi Musa Ɗankwaro ke faɗi, ‘Ba Fansho Ba Garatuti.’

Kamar yadda muka faɗa a sama, abin farin cikin shi ne yadda Hukumomi a Jami’o’i da gwamnatoci ke ɗaukar abin da muhimman a yanzu fiye da a da, wanda ɗaliba ba ta da wani abin yi, ko dai ta ba da kai bori ya hau ko kuma ta rasa karatun.

Wani abin farin ciki shi ne a shekarun baya Majalisar Dattawan ƙasar nan ta gabatar da wani ƙuduri mai zafin gaske da zai daƙile yawaitar irin wannan cin zarafin da ake yi wa mata a Jami’o’i.

Wannan dokar da za ta taimaka wajen daƙile yawaitar wannan cin zarafin mata ta nau’o’i daban-daban, walau ko ta tursasa musu a yi zina da su don a ba su maki, ko karɓar kuɗaɗensu, ko wasu hanyoyi, idan an samu nasarar dokar, za ta taimaka wajen wa ɗalibai a manyan makarantun da suke ƙasar nan.

Wannan dokar tana zuwa ne a daidai lokacin da ƙorafe-ƙorafe ya yi yawa game da wannan lamari, wanda kuma kowa na ammannar cewa idan har aka tabbatar da ita, to za ta taimakawa ’ya’yan jama’a.

A cikin tanadin wannan doka da Majalisar ta gabatar, an ware wa’adin shekaru har 14 a kurkuku ga duk Malamin da aka cafke yana lalatada wata ɗaliba a duk faɗin ƙasar nan, ba tare da wani zaɓi na biyu ba.

Ƙudurin wanda ya zarce karatu na ɗaya da na biyu a Majalisar Dattawan, Mataimakin Shugaban Majalisar, ya gabatar da shi, da fatan idan ya zama doka zai kawo ƙarshen wannan cin zarafin.