15
Feb
Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa ganawarsa da Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ba ta haifar da wata yarjejeniya tabbatacciya ba dangane da batun Iran, sai dai an amince da ci gaba da tattaunawa. Wannan shi ne karo na bakwai da shugabannin biyu suka gana cikin watanni 13 da suka gabata. Trump ya jaddada cewa, duk wata yarjejeniya dole ta tabbatar da cewa Iran ba za ta mallaki makamin nukiliya ko makamai masu linzami ba. Isra’ila na son tattaunawar ta wuce batun nukiliya kadai ta hada da makaman ballistic da kuma goyon bayan ƙungiyoyin da take ɗauka a matsayin barazana.…
