Sojoji sun kifar da gwamnatin Bazoum

Daga BASHIR ISAH

Sojoji a ƙasar Nijar sun yi wa Shugaban Ƙasar, Mohamed Bazoum, juyin mulki ranar Laraba da daddare sa’o’i bayan da masu tsaronsa suka tsare shi a fadarsa.

A jawabin da ya yi wa ‘yan ƙasa kai tsaye a tashar talabijin ta ƙasar, Colonel-Major Amadou Abdramane ya bayyana cewa, “sojoji da sauran hukumomin tsaro sun yanke shawarar jawo ƙarshen gwamnatin da kuka sani.

“Wannan ya biyo bayan ci gaba da taɓarɓarewar tsaron ƙasar da kuma rashin walwala da ingancin tattalin arziki,” in ji shi.

Sojojin sun ce an rufe iyakokin ƙsar, sannan an kafa dokar hana zirga-zirga a ƙasa baki ɗaya, haka ma an dakatar da duka cibiyoyin ƙasar.

An ga Abdramane zaune yayin da wasu manyan jami’an sosjiji guda tara suka take masa baya a lokacin da yake jawabin nasa.

Sojojin da ke da hannu a juyin mulkin sun gargaɗin kada wanni ko wasu su yi tunanin tsoma baki cikin batun daga ƙetare.