Kasashen Waje

Mutum 16 sun mutu sakamakon shaƙar iskar gas a Afirka ta Kudu

Mutum 16 sun mutu sakamakon shaƙar iskar gas a Afirka ta Kudu

Daga BASHIR ISAH Rahotanni daga ƙasar Afirka ta Kudu sun ce, wasu mutum 16 sun mutu sakamakon shaƙar iskar gas. An danganta lamarin wanda ya auku a ranar Laraba a Boksburg da ke gabashin Johannesburg, da yoyon tukunyar gas a yankin. Bayanai sun nuna an samu yoyon tukunyar gas ɗin ne sakamako haramtattun ayyukan masu haƙar zinari a yankin. Jami'an yankin sun ce waɗanda lamarin ya shafa sun haɗa da mata da ƙananan yara. Kazalika, sun ce samfurin gas ɗin da ya yi wannan ta'asar, wato 'Nitrate oxide gas', galibi da shi masu haƙar ma'adinai ta haramtacciyar hanya ke amfani…
Read More
Hajjin 2023: Nijeriya ta buƙaci kamfani ya maido da kuɗin da aka biya shi saboda rashin ingancin aiki

Hajjin 2023: Nijeriya ta buƙaci kamfani ya maido da kuɗin da aka biya shi saboda rashin ingancin aiki

Daga BASHIR ISAH Hukumar Aikin Hajji ta Nijeriya, NAHCON, ta buƙaci kamfanin da ya yi wa mahajjatan Afirka daga ƙasashen da ba Larabawa ba hidima yayin Hajjin bana a Saudiyya, da ya maido da kuɗaɗen da aka biya shi. NAHCON ta buƙaci hakan daga Kamfanin Mutawifs for Pilgrims from Africa Non-Arab Countries ne saboda gazawar kamfanin wajen yi wa alhazan Nijeriya hidima yadda ya kamata a Mina yayin aikin Hajjin 2023. Shugaban NAHCON na ƙasa, Zaikrullah Kunle Hassan, tare da wakilan hukumomin alhazai na jihohi da kamfanonin yawon buɗe ido su ne suka buƙaci hakan bayan da suka nuna rashin…
Read More
An kama mutum 2000 kan tada tarzoma a Faransa

An kama mutum 2000 kan tada tarzoma a Faransa

Rahotanni daga ƙasar Faransa sun ce, sama da mutane dubu biyu ne aka kama a Faransa, tun bayan tarzomar da ta biyo bayan kisan da 'yan sanda suka yi wa matashi Nahel. Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida ta Ƙasar ce ta bayyana haka a ranar Lahadi. Zanga-zangar wadda aka shafe kimanin kwana biyar ana gudanar da ita, hukumomin Faransa sun tabbatar da kama mutane 719 a ranar Asabar. Ma’aikatar ta ƙara da cewa ana samun raguwar tarzomar da aka faro tun a ranar Talatar da ta gabata. Ministan Kulada Harkokin Cikin Gida na Faransa, Gerald Darmanin, ya sanar a ranar Asabar…
Read More
Za a fassara Huɗubar Arfar bana da harshen Hausa a Saudiyya

Za a fassara Huɗubar Arfar bana da harshen Hausa a Saudiyya

Daga BASHIR ISAH Hukumomin Saudiyya sun bayyanar da harsunan da za a fassara Huɗubar Arfa yayin aikin Hajjin 2023. Sanarwar hukumomin ta nuna manyan harsunan duniya guda 20 ne za a fassara huɗubar a cikinsu, ciki har da harshen Hausa. Shugaban kula da masallacin Ka'aba da na Annabi da ke Madina, Sheikh Dr. Abdulrahman Al-Sudais ne ya bayyana haka, yana mai cewa an kammala dukkan shirye-shirye domin yaɗa huɗubar kai tsaye daga Masallacin Namirah. A cewarsa, harsunan da lamarin ya shafa sun haɗa da: Hausa, Faransanci, Ingilishi Persian, Urdu, Russian, Turkish, Punjabi, Sinan i, Malayo, Swahili, Spanish, Portuguese, Amharic, Jamussanci,…
Read More
Shugabannin Afrika sun miƙa kukansu a taron Paris

Shugabannin Afrika sun miƙa kukansu a taron Paris

Shugabannin ƙasashen Nijar Benin da kuma Ghana sun miƙa kokensu ga taron yanayin da ke gudana a birnin Paris kan yadda manyan ƙasashe ke mayar da hankali wajen zuba maƙuden kuɗi a Ukraine ba tare da duba halin da nahiyar Afrika ke ciki ba, koken da ke zuwa a dai dai lokacin da Amurka ta sanar da shirin zuba ƙarin dala biliyan 1 da miliyan 300 don farfaɗo da tattalin arzikin ƙasar mai fama da yaqi. Shugabannin ƙasashen na Ghana Benin da kuma jamhuriyyar Nijar yayin jawabinsu gaban taron yanayin wanda ke ci gaba da gudana a birnin Paris na…
Read More
Sama da baƙin haure 70 sun ɓace a gaɓar ruwan Girka

Sama da baƙin haure 70 sun ɓace a gaɓar ruwan Girka

Aƙalla mutane 78 ne suka mutu inda ake fargabar da dama sun ɓace, bayan da wani ƙaramin jirgin ruwa ɗauke da baƙin haure ya kife a ruwa a Ƙasar Girka, hatsari mafi muni da ya auku a wannan shekara, inji MƊD. Kwale-kwalen wanda ya nutse a kudancin gaɓar tekun Girka, mai nisan kilomita 87 daga kudu maso yammacin Pylos, hukumomi sun ce masu aikin ceto sun fuskanci ƙalubale sakamakon kakkafar iska da ta kunno kai. Yanzu haka dai kusan mutum 100 aka samu nasarar cetowa, inda ake ci gaba da laluben waɗanda suka ɓata. An dai yi amfani da jirage…
Read More
Rashin lafiya zata yi sanadin sakin wanda ake zargi da kisan kiyashi a Rwanda

Rashin lafiya zata yi sanadin sakin wanda ake zargi da kisan kiyashi a Rwanda

Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC, ta ce Felicien Kabuga, da ke fuskantar tuhuma bisa zargin yana da hannu a kisan kiyashin Rwanda cewa ba shi da isasshiyar lafiyar da zai fuskanci tuhuma. Kotun ta ce za ta yi amfani da wata dokar wacce za ta yi kamanceceniya da shari’ar da ake wa Kabuga mai shekaru 80, amma ba za ta yanke masa hukunci ba. Alƙalai a kotun da ke Hague sun ce Kabuga, wanda ake ce-ce-ku-ce kan takamaiman ranar haihuwarsa, da wuya ya sake samun isasshiyar lafiya a nan gaba. An yanke shawarar ne bayan likitoci sun gano…
Read More
An sallami Shugaban kafar yaɗa labarai ta CNN

An sallami Shugaban kafar yaɗa labarai ta CNN

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban Warner Bros. Discovery, kamfanin da ke mallakar CNN, David Zaslav, ya sanar da sallamar Chris Licht ne kwana biyu bayan Licht ya shaida wa ma’aikata a lokacin taron editoci cewa zai yi duk abin da zai iya don samun yardar mutanen da ke kusa da shi. Zaslav ya sanar da sallamar Licht ne daidai lokacin da CNN ke fama da raguwar masu kallo da kuɗaɗen shiga, ga kuma yawan kurakurai a cikin shirye-shiryen da kafar take gabatarwa. Adadin mutum 494,000 da ke kallon CNN a lokaci manyan shirye-shiryensa a watan Afrilu, ya ragu…
Read More
An kashe Gwamnan Afghanistan a harin bom

An kashe Gwamnan Afghanistan a harin bom

Daga BASHIR ISAH Rahotanni daga yankin Arewacin Afghanistan sun ce, an kashe gwamnan riƙo na yankin a wani harin bom da aka kai ta hanyar amfani da mota. Wannan shi ne makamancin harin da aka yi amfani da shi wajen kashe wani babban jami'in ɗan sanda a yankin, harin da mayaƙan ISIL (ISIS) suka ɗauki alhakin kaiwa. An ce maharin ya shigi motar Nisar Ahmad Ahmadi da motarsa mai ɗauke da bom wanda hakan ya yi sanadiyar mutuwar muƙaddashin gwamnan Arewacin Badakhshan a ƙasar. Bayanai sun ce direban motar ya mutu yayin da wasu mutum shida sun jikkata. Ya zuwa…
Read More
An cafke tsohuwar shugabar makaranta da laifin yi wa ɗalibai fyafe

An cafke tsohuwar shugabar makaranta da laifin yi wa ɗalibai fyafe

An samu wata tsohuwar shugabar makaranta, 'yar asalin Isra’ila da laifin cin zarafin wasu ɗalibanta biyu a wata makarantar Yahudawa da ke Australia. Kotu a birnin Melbourne na Australia ta samu Malka Leifer da laifin cin zarafin wasu yara mata guda biyu Dassi Erlich da Elly Sapper tsakanin shekarun 2003 zuwa 2007. Sai dai, ba a same ta da laifin yin lalata da yarinya ta uku da aka tuhume ta a kai ba, Nicole Meyer. Leifer, mai shekara 56 ta musanta zarge-zargen da aka yi mata tun da farko, kuma ta kwashe shekaru tana ƙoƙarin ganin ba a mayar da…
Read More