Kasashen Waje

Isra’ila da Islamic Jihad sun yi wa juna ruwan makaman roka cikin dare

Isra’ila da Islamic Jihad sun yi wa juna ruwan makaman roka cikin dare

Sojojin Isra’ila da mayaƙan Islamic Jihad a yankin Gaza sun sake shafe tsawon dare suna kai wa juna hare-haren manyan makamai dai dai lokacin da alƙaluman Falasɗinawan da aka kashe cikin kwanaki 2 da faro rikicin ke tasamma 22. Rikicin wanda ke matsayin mafi muni da aka gani tsakanin ɓangarorin biyu a watannin baya-bayan nan kowanne ɓangare na ci gaba da harba makaman roka ta yadda babu abin da ake jiyowa sai ƙarar harbawa da kuma tarwatsewarsu, kamar yadda majiyoyin labaran da ke sanya idanu kan rikicin ke bayyanawa a wani yanayi da Masar ke shige da fice don ganin…
Read More
Ingila ta yi sabon Sarki bayan shekaru 70

Ingila ta yi sabon Sarki bayan shekaru 70

*Sarki Charles na III ya gaji mahaifiyarsa Rahotanni daga ƙasar Ingila sun ce, an gudanar da gagarumin bikin naɗin Sarki Charles na III a wannan Asabar, inda Arcbishop na Canterbury ya sanya masa kambin sarautar Ingila domin maye gadon mulki na marigayiya Sarauniya Elizabeth ta biyu. Bikin, shi ne irinsa na farko cikin shekaru 70 da suka gabata. An gani tare da jin yadda mahalartar bikin suka ɓige da sowa a yayin sanya wa Sarkin kambin sarauta na zinari wanda aka samar da shi tun a ƙarni na 17. Tun bayan da aka gudanar da makamancin wannan biki a shekarar…
Read More
Tattaunawa ce kaɗai mafita tsakanin Rasha da Ukraine – Chana

Tattaunawa ce kaɗai mafita tsakanin Rasha da Ukraine – Chana

Shugaban Ƙasar Chana Xi Jinping, ya tattauna da takwaransa na Ukraine Volodymyr Zelensky ta wayar tarho, kamar yadda fadar gwamnatocin ƙasashen biyu suka tabbatar, wanda shi ne kira na farko da shugabannin biyu suka yi tun bayan kaddamarwa ƙasar da Rasha ta yi. "Na yi doguwar tattaunawa mai ma'ana ta wayar tarho tare da shugaba Xi Jinping," inji Zelensky a shafin Twitter. "Na yi imanin cewa, wannan tattaunawa da aka yi, da kuma naɗa jakadan Ukraine a Ƙasar Chana, za su ba da ƙwarin gwiwa wajen raya dangantakar da ke tsakanin ƙasashen biyu." Mai magana da yawun Zelensky Sergiy Nykyforov,…
Read More
Tilas maniyyata su yi allurar Korona kwanaki 10 kafin a fara aikin Hajji — Saudiyya

Tilas maniyyata su yi allurar Korona kwanaki 10 kafin a fara aikin Hajji — Saudiyya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ma’aikatar Hajji da Umrah ta ƙasar Saudiyya ta bayyana cewa ranar ƙarshe da maniyyata za su yi allurar rigakafin Korona ita ce kwanaki 10 kafin lokacin fara aikin Hajji. Yin allurar rigakafin sharaɗi ne da zai ba su damar gudanar da aikin Hajji. Hakan ya zo ne yayin da ma’aikatar ta amsa wa wani mutum tambaya a shafin ta na Tuwita. Mutumin ya yi tambaya ko yin allurar Korona kashi na uku wani sharaɗi ne na yin aikin Hajji. Ma’aikatar ta fayyace cewa kammala dukkan kashi na allurar rigakafin ya zama tilas wajen bayar…
Read More
Manyan sojojin Sudan sun amince da tsagaita wuta na sa’o’i 72

Manyan sojojin Sudan sun amince da tsagaita wuta na sa’o’i 72

Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya, Antony Blinken, ya bayyana cewa, manyan sojojin Sudan sun amince da tsagaita wuta na kwana uku daga ranar Talata. Blinken ya ce, “Biyo bayan tattauna mai zafi na sa'o'i 48, Rundunar Sojojin Sudan (SAF) da Rundunar RSF sun amince da matakin tsagaita wuta a faɗin ƙasar na sa'o'i 72 hours." Ya karatda cewa, “Amurka ta yi kira ga SAF da RSF da su tabbatar da tsagaita wutar nan take kamar yadda aka cimma." Haka nan, ya ce Amurka na aiki tare da abokan hulɗa don kafa kwamitin da zai tattauna batun tabbatar da tsagaita wuta na…
Read More
Rikicin Sudan: Saudiyya ta zama ƙasa ta farko wajen kwashe ‘ya’yanta

Rikicin Sudan: Saudiyya ta zama ƙasa ta farko wajen kwashe ‘ya’yanta

Daga BASHIR ISAH Wani jirgin ruwan Ƙasar Saudiyya ya isa Jidda bayan da ya yi jigilar 'yan ƙasar da suka maƙale a Ƙasar Sudan sakamakon rikicin da ƙasar ke fama da shi. A cewar tashar talabijin ta Jidda, “Jirgin ruwan farko da ya kwaso 'yan ƙasar daga Sudan ya isa gida ɗauke da mutum 50 tare da wasu daga maƙwabtan ƙasar." Bayanai sun ce an hangi wasu jiragen ruwa na ƙasashe daban-daban a Kogin Maliya ɗauke da mutum 108 daga Sudan wanda ake sa ran su isa ƙasashensu ba da jimawa ba. Wannan nasarar da Saudiyya ta samu ya sa…
Read More
Har yanzu ban dawo hayyacina ba kan abinda Hakimi ya min – Hiba

Har yanzu ban dawo hayyacina ba kan abinda Hakimi ya min – Hiba

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Matar Achraf Hakimi, ɗan ƙwallon ƙungiyar PSG kuma ɗan asalin ƙasar Moroko, wato Hiba Abouk, ta ce, abinda Hakimi ya mata ta kadu sosai, wanda hakan ya sa har yanzu ba ta dawo hayyacinta ba. A shekarar 2020 ne dai suka yi aure da Hakimi inda a yanzu suna da yara biyu, amma sun rabu, matar ta nemi Hakimi ya ba ta rabin dukiyarsa, amma sai lauyanta ya gano Hakimi da sunan mahaifiyarsa ya ke ajiye kadarorinsa. A zantawar da ta yi da kafar Elle, Hiba ta bayyana cewa rabuwarsu ba abu ne me sauƙi ba…
Read More
Indiya ta zarta Chana da yawan jama’a

Indiya ta zarta Chana da yawan jama’a

Indiya za ta wuce Chana a matsayin qasa mafi yawan jama'a a duniya a ƙarshen watan Yuni, alqalumman Majalisar Ɗinkin Duniya sun nuna cewa, hakan zai haifar da babban qalubale ga ƙasar da ke ƙoƙarin samar da ababen more rayuwa daidai lokaccin da ta ke fama da rashin isassun ayyukan yi ga miliyoyin matasa. Alqaluman sun nuna cewa, yawan al'ummar Indiya ya kai sama da biliyan 1.400 inda ya haura adadin yawan al’ummar Ƙasar Chana da miliyan uku, wanda ke da adadin sama da mutum biliyan ɗaya, inji rahoton hukumar kula da yawan jama’a ta Majalisar Ɗinkin Duniya. A baya…
Read More
Saudiyya ta kama ‘yan ci-rani sama da 16,000

Saudiyya ta kama ‘yan ci-rani sama da 16,000

Hukumomin Saudiyya sun ce sun kama baƙin haure 16,407 da suka shiga ƙasar ba bisa ƙa'ida ba, a yankuna daban-daban na ƙasar cikin mako ɗaya. Jaridar Saudi Gazette ta ambato ma'aikatar harkokin cikin gida ta ƙasar na cewa an kama mutanen ne bayan wani samamen haɗin gwiwa da jami'an tsaro suka ƙaddamar a sassa daban-daban cikin wannan wata na Ramadan. Kamen ya haɗa da mutunen da suke zaune a ƙasar ba tare da izini ba, da mutunen da ba su da takardun shiga ƙasar, sai kuma mutunen da suka sava ƙa'idojin aiki na Saudiyya. Ma'aikatar ta ce ta kama wasu…
Read More
Donald Trump ya gurfana gaban kotu, ya musanta zargin da ake yi masa

Donald Trump ya gurfana gaban kotu, ya musanta zargin da ake yi masa

Tsohon Shugaban Ƙasar Amurka, Donald Trump, ya musanta zarge-zargen laifuka 34 da ake tuhumar sa da aikatawa, bayan wani bincike da ya gano cewa ya bai wa wata jarumar fina-finan batsa mai suna Stormy Daniels, toshiyar baki. Trump wanda ya miƙa kansa ga Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Amurka da ke Manhattan, shi ne Shugaban Ƙasar na farko da ya fara fuskantar tuhuma da ta danganci aikata manyan laifuka. Rahotanni na nuni da cewa, Trump ya ba wa jarumar fina-finan batsar kuɗin toshiyar bakin ne a shekarar 2016. Bayan da ya bayyana gaban kotu, tsohon shugaban na Amurka ya wallafa…
Read More