Indiya za ta wuce Chana a matsayin qasa mafi yawan jama’a a duniya a ƙarshen watan Yuni, alqalumman Majalisar Ɗinkin Duniya sun nuna cewa, hakan zai haifar da babban qalubale ga ƙasar da ke ƙoƙarin samar da ababen more rayuwa daidai lokaccin da ta ke fama da rashin isassun ayyukan yi ga miliyoyin matasa.
Alqaluman sun nuna cewa, yawan al’ummar Indiya ya kai sama da biliyan 1.400 inda ya haura adadin yawan al’ummar Ƙasar Chana da miliyan uku, wanda ke da adadin sama da mutum biliyan ɗaya, inji rahoton hukumar kula da yawan jama’a ta Majalisar Ɗinkin Duniya.
A baya dai ana kallon Chana a matsayin ƙasa mafi yawan al’umma a duniya tun bayan faɗuwar daular Rum, amma a bara yawan al’ummarta ya ragu a karon farko tun 1960, yayin da na Indiya ke ci gaba da ƙaruwa.
Qasar da ta kasance mafi girma a Kudancin Asiya ta bazu daga yankin Himalaya zuwa bakin teku na Kerala, ana amfani da harsunan har guda 22, kuma kusan rabin mazauna yankin ba su haura shekaru 25 da haihuwa.
Ƙasar na fuskantar manyan ƙalubale wajen samar da wutar lantarki da abinci da gidaje ga al’ummarta, inda da yawa daga cikin manya-manyan garuruwan ƙasar sun jima suna fama da matsalar ƙarancin ruwa, gurɓacewar iska da ruwa, da kuma matsuguni.
A cewar cibiyar bincike ta Pew, adadin mutanen Indiya ya ƙaru da fiye da biliyan ɗaya tun daga 1950, shekarar da Majalisar Ɗinkin Duniya ta fara tattara bayanan yawan jama’a.
Ƙasar Chana ta kawo ƙarshen tsauraran manufofinta na ƙayyade haihuwa, wanda aka sanya a shekarar 1980 lokacin da ta ke fargabar yawan al’ummarta za su ninka a shekarar 2016, sai dai daga bisani ta fara barin ma’aurata su haifi ‘ya’ya uku a shekarar 2021.