Har yanzu ban dawo hayyacina ba kan abinda Hakimi ya min – Hiba

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Matar Achraf Hakimi, ɗan ƙwallon ƙungiyar PSG kuma ɗan asalin ƙasar Moroko, wato Hiba Abouk, ta ce, abinda Hakimi ya mata ta kadu sosai, wanda hakan ya sa har yanzu ba ta dawo hayyacinta ba.

A shekarar 2020 ne dai suka yi aure da Hakimi inda a yanzu suna da yara biyu, amma sun rabu, matar ta nemi Hakimi ya ba ta rabin dukiyarsa, amma sai lauyanta ya gano Hakimi da sunan mahaifiyarsa ya ke ajiye kadarorinsa.

A zantawar da ta yi da kafar Elle, Hiba ta bayyana cewa rabuwarsu ba abu ne me sauƙi ba musamman kasancewa da ’ya’ya a tsakaninsu.

Ta ce, abu ne wanda sai a hankali za ta dawo daidai daga kaɗuwar da ta ke ciki.

Abouk da Hakimi suna da ‘ya’ya biyu, Amin, ’yar shakara 3, da Naim, 1, tare bayan da ma’auratan suka yi aure a 2020, shekaru biyu bayan haɗuwa a 2018.

Da ta ke magana da ELLE a ranar Laraba, Abouk ta ce, “Ina lafiya, amam akwai lokutan da nake shiga firgici, domin lamarin ya buge ni sosai, lamari ne mai rikitarwa, sai ya ɗauki lokaci kafin in dawo daidai”.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *