Saudiyya ta kama ‘yan ci-rani sama da 16,000

Hukumomin Saudiyya sun ce sun kama baƙin haure 16,407 da suka shiga ƙasar ba bisa ƙa’ida ba, a yankuna daban-daban na ƙasar cikin mako ɗaya.

Jaridar Saudi Gazette ta ambato ma’aikatar harkokin cikin gida ta ƙasar na cewa an kama mutanen ne bayan wani samamen haɗin gwiwa da jami’an tsaro suka ƙaddamar a sassa daban-daban cikin wannan wata na Ramadan.

Kamen ya haɗa da mutunen da suke zaune a ƙasar ba tare da izini ba, da mutunen da ba su da takardun shiga ƙasar, sai kuma mutunen da suka sava ƙa’idojin aiki na Saudiyya.

Ma’aikatar ta ce ta kama wasu a lokacin da suke ƙoƙarin tsallaka kan iyakar ƙasar, wasu kuma an kama su ne lokacin da suke yunƙurin fita daga ƙasar .

Ta ce, kashi 74 na waɗanda aka kama, ‘yan Habasha ne, sai kashi 22 ‘yan asalin Yemen, kashi huɗu kuma na sauran ƙasashe.

Ma’aikatar cikin gidan ta ce an tura ‘yan ci-rani 6,251 zuwa ofisoshin jakadancin ƙasashensu da ke Saudiyya don samar musu takardun izini, yayin da za a mayar da mutum 10,156 zuwa ƙasashen da suka fito.

Ta dai gargaɗi duk wani mutum da ya yi sanadin shigar da wani baƙon haure cikin Saudiyya ba bisa ƙa’ida ba, ko ya ba shi masauki, ko aiki, da dai duk wani nau’in taimako, ya tabbatar cewa zai fuskanci hukuncin da zai iya kai wa ɗaurin shekara 15 a gidan yari, matuƙar aka kama shi.

Sannan da biyan tarar Riyal miliyan ɗaya, idan aka same shi da laifin haɗa baki wajen shigar da baƙin haure cikin ƙasar, da kuma samar musu masauki.