Hukumar tsaro ta DSS ta cika hannu da fitaccen fasto a filin jirgin sama da ke Legas.
A ranar Juma’a jami’an tsaro suka kama tare da tsare Apostle Tomi Arayomi a Legas.
Ɗan uwansa, Tobi Arayomi, shi ne ya bayyana haka a shafinsa na Instagram mai taken @tobiarayomi da misalin karfe 12 na rana.
A cewar Tobi, jami’an DSS sun yi ram da ɗan uwan nasa ne kan hasashen da ya yi game da sha’anin siyasa.
Tobi ya wallafa a shafin nasa cewa, “….Ina buƙatar taimakonku. Yanzu na samu labarin jami’an DSS sun kama ɗan uwana a Nijeriya.
“An tsare shi ne bisa dalilai na siyasa, tare da matarsa, Tema, aka kama su.
“Saukarsa Legas ke nan aka kama shi a filin jirgin sama. Ana bibiyarsa ne saboda hasahen da ya yi ya zame wa gwamnati Nijeriya abin damuwa,” in ji Tobi.
A baya, wanda lamarin ya shafa ya yi hasashe a lokuta mabambanta game da zaɓukan Nijeriya na 2023 da kuma sakamakonsu.
Gabanin zaɓen na 2023, Faston ya yi hasashen ɗan takarar shugabancin ƙasa na Jam’iyyar APC, Bola Tinubu ne zai lashe zaɓen Shugaban Ƙasa da dai sauransu.