Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe
Sabon zaɓaɓɓen ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazaɓar Gombe/Kwami/Funakaye, Injiniya Usman Maijama’a Kallamu, ya yi alƙawarin mayar da ayyukan ci gaba da ingantaccen wakilci cikin abubuwan da zai fi bai wa muhimmanci a sauran wa’adinsa a majalisar dokoki ta ƙasa.
Kallamu ya bayyana hakan ne bayan ya samu nasara a zaɓen cike gurbin kujerar mazaɓar da aka gudanar a ranar 19 ga Satumba.
Ya ce zai mayar da hankali wajen jawo ayyuka da shirye-shiryen tallafi da za su taimaka wajen magance matsalolin da al’ummomin ƙananan hukumomin Gombe, Kwami da Funakaye ke fuskanta.
A cewarsa, nasarar da ya samu ba wai kawai nasarar siyasa ba ce, illa amanar da al’umma suka ɗora masa domin yi musu hidima da kuma samar da shirye-shiryen da za su inganta rayuwarsu.
“Zan yi amfani da sauran lokacin da ya rage na wa’adina wajen bibiyar ayyuka da shirye-shiryen da za su kawo ci gaba kusa da jama’a. Babban abin da zan mayar da hankali a kai shi ne ingantaccen wakilci da tabbatar da cewa jama’a sun ga amfanin wannan dama da suka ba ni,” in ji shi.
Kallamu ya ce zai haɗa kai da hukumomin gwamnati da abin ya shafa, masu ruwa da tsaki da shugabannin al’umma domin gano muhimman buƙatun mazaɓar tare da ganin an samar da ayyukan da suka dace.
Ya kuma yi kira ga al’ummar ƙananan hukumomin ukun da su ci gaba da kasancewa cikin haɗin kai, yana mai tabbatar musu da cewa buƙatunsu za su kasance a sahun gaba a ayyukansa na majalisa.
Ɗan majalisar ya gode wa masu kaɗa ƙuri’a bisa amanar da suka ba shi, yana mai bayyana nasarar tasa a matsayin nasarar al’umma baki ɗaya.
Ya kuma yaba wa Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, shugabannin jam’iyyar APC da sauran masu ruwa da tsaki bisa irin goyon bayan da suka ba shi, tare da gode wa ’yan jam’iyyar, ƙungiyoyin yaƙin neman zabe, sarakunan gargajiya, shugabannin al’umma da magoya bayansa da suka bayar da gudunmawa wajen samun nasarar.
Kallamu ya kuma tabbatar wa al’ummar mazaɓar cewa zai kasance mai sauƙin samu kuma mai jajircewa wajen tabbatar da ingantaccen wakilci, yana mai cewa zai yi ƙoƙarin ganin ya cancanci amanar da suka ɗora masa.
Ya lashe zaɓen cike gurbin da aka gudanar a ranar 19 ga Satumba domin maye gurbin tsohon ɗan majalisar, Honarabul Yaya Bauchi Tongo, wanda ya rasu.
