Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Uwar gidan Gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ta taya uwar gidan shugaban ƙasan Najeriya, Sanata Oluremi Tinubu, CON, murna a bikin cikarta shekaru 66.
A cikin wani saƙon fatan alheri da sakatariyar yaɗa labarai, Rabi Yusuf, ta fitar a Hajiya Huriyya tace tabi sahun miliyoyin ‘yan Najeriya a gida da kuma a ƙasashen waje don taya uwar gidan shugaban ƙasa Remi Tinubu murnar cika shekara 66 da haihuwa
Hajiya Huriyya ta bayyana Sanata Oluremi Tinubu a matsayin uwa mai tausayi kuma shugaba wacce ta sadaukar da rayuwarta a cikin hidimar jama’a.
Hajiya Huriyya ta bayyana ywar gidan shugaban ƙasan a matsayin mace wadda ta sadaukar da rayuwar ta ta hanyar jajircewa ga walwalar mata, yara da sauran ƙungiyoyi masu rauni a faɗin ƙasar.
Ta yaba wa Sanata Tinubu bisa jagoranci mai tasiri da kuma ƙoƙarinta na ci gaba da ƙirƙirar damammaki masu ma’ana da inganta rayuwar ‘yan ƙasa da kuma shirye-shiryen ƙarfafawa daban-daban.
A cewar sanarwar, Hajiya Huriyya ta lura cewa sadaukarwar uwar gidan shugaban ƙasan ya bada fifikon gaske ga gina ƙasa da ayyukan jin ƙai na ci gaba da zaburar da mata a fannin shugabanci da kuma matasan Najeriya.
Hajiya Huriyya Dauda Lawal ta yi addu’ar Allah ya ci gaba da ba wa uwar gidan shugaban ƙasa lafiya da ƙarfi a cikin hidimar ta ga alummar Najeriya.
“Ina tare da miliyoyin mutane a faɗin ƙasar nan da ma waɗanda suke a wajen Najeriya tare da girmama uwar gidan shugaban ƙasa wace ta sadaukar da rayuwar ta domin ƙarfafawa da kuma ɗaga darajar mutane da yawa. Allah ya ƙara mata lafiya, hikima da zaman lafiya.” Cewar Hajiya Huriyya
