Kashe-kashen Filato: Gwamnatin jihar ta sanya dokar kulle a ƙananan hukumomi uku

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamnatin Jihar Filato ta sanar da sanya dokar hana fita da dare a sassan ƙananan hukumomin Barikin Ladi, Ɓokkos da Mangu a sakamakon matsalolin tsaro da suka shafi wasu ƙauyukansu.

Dokar, wadda ta fara daga ranar Litinin, 21 ga Satumba, 2026 ta umarci mazauna ƙananan hukumomin da su zauna a gidajensu daga tsakanin ƙarfe 6 na yamma zuwa 6 na safe har illa ma sha Allahu.

Kwamishinar Yaɗa Labaran jihar, Joyce Lohya Ramnap ce ta sanar da haka a wata sanarwa, inda ta ce an ɗauki matakin ne domin bai wa jami’an tsaro damar dawo da ɗorewar al’amura a yankunan da rashin tsaro ya shafa, bayar da kariya ga rayuka da kuma hana karya doka da oda. Masanin harkar tsaro, Zagazola Makama a nasa ɓangaren, ya ruwaito cewa Lohya ta bayyana cewa ana tsammanin mazaunan su kasance masu biyayya ga umarnin da kuma shirya tare da tsara gudanar da harkokinsu cikin sa’o’in da dokar ba ta shafa ba.

Haka kuma, gwamnatin ta umarci jami’an hukumomin tsaro da su tabbatar da cikakken biyayya ga dokar a sassan ƙananan hukumomi ukun. Sannan ta haramta amfani da babura a yankunan da al’amarin ya shafa a matsayin ɓangare na warware matsalolin tsaron, tana mai tabbatar wa al’umma cewa za ta tura ƙarin wasu jami’ai domin ganin an aiwatar da dokar yadda ta dace.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Jihar Filato ke fuskantar hare-hare da mayar da martani acikin al’umma a sassanta musamman a Barikin Ladi, Ɓokkos da Mangu, lamarin da ya tilasta wa gwamnatin ƙara tura wani adadi na jami’an tsaro da tawagogin sintiri zuwa yankunan domin daƙile cigaba da aukuwar wasu rikice-rikice.

Makama ya kuma ruwaito cewa, sojoji sun yi nasarar daƙile wani harin ramako da aka yi zargin mayaƙan Fulani da yunƙurin ƙaddamarwa bayan kisan wani ɗan yankin Barkin Ladi. Hakan ya biyo baya wasu rikice-rikice da aka ƙaddamar a ƙauyukan Ɗorawan Babuje, Sherum, Maraban Kantoma da Lajam duk a ƙaramar hukumar.

By Babaji

Leave a Reply