Mutuwar ‘yan Neja 37: Zainab Okino ta Blueprint ta samu gurbi yayin da Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da kwamitin bincike

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamnatin Tarayya ta kafa kwamitin bincike mai zaman kansa na mutum goma domin gaggauta gudanar da bincike akan ainihin dalilan da suka sabbaba mutuwar mutane 37 da ake zargin masu haƙar ma’adinai ne ba bisa doka ba a Jihar Neja.

Da yake ƙaddamar da kwamitin a Abuja, Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya ce gwamnatin tarayyar ta duƙufa wajen ganin an yi wa mamatan adalci, waɗanda suka rasu a ofishin Hukumar Sibil Difens (NSCDC) reshen Jihar Neja.

An bai wa kwamitin, wanda tsohon Mataimakin Darakta-Janar na Hukumar Tsaro ta Farin kaya (DSS), Jonathan Kure yake jagoranta tare da tsohon Darakta-Janar na Makarantar Koyon Aikin Shari’a ta Nijeriya (NLS), Farfesa Isa Hayatu Chiroma (SAN) a matsayin sakatare, mako biyu kacal domin ya gabatar da rahoton abin da ya gano akan al’amarin.

Sauran mambobin kwamitin sun haɗa da AIG Hosea Hassan Karma (mai ritaya); Farfesa Olayinka Buhari, wanda farfesa ne a sashen nazarin cutuka masu kisa kuma tsohon Babban Daraktan Lafiya a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ilorin; sai wakili daga Majalisar Masarautar Minna da wakili daga Gwamnatin Jihar Neja. Haka kuma, akwai Alhaji Liman Sulaiman, Sakataren Ƙungiyar Masu Haƙar Ma’adinai ta Ƙasa;
Lauya kuma mai fafutukar kare ‘yancin ɗan-adam, Deji Adeyanju; Misis Zainab Suleiman Okino ta jaridar Blueprint; da kuma mai sharhi kan harkokin al’umma, Dakta George Agbakahi.

A jawabinsa, ministan ya yi godiya ga Shugaba Bola Tinubu bisa samar da kwamitin da kuma umartar a yi bincike kan al’amarin, yana mai cewa hakan ɓangare ne na ƙoƙarin tabbatar da adalci ga mamatan. Tunji-Ojo ya kuma miƙa gaisuwar ta’aziyyarsa ga iyalansu da kuma kira da su kwantar da hankali yayin da ake gudanar da bincike akan al’amarin.

Mutane 37 ne dai da aka tsare suka rasu a ranar Alhamis, 17 ga Satumba, 2026, a ofishin NSCDC reshen Jihar Neja, kamar yadda Manhaja ta ruwaito a baya. Har zuwa yanzu dai ba a tabbatar da ainihin abin da ya sabbaba mutuwarsu ba yayin da hukumomi suka umarci a yi bincike domin gano haƙiƙanin yadda al’amarin ya auku.

By Babaji

Leave a Reply