
Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya amince da biyan Naira biliyan 3.659 ga ‘yan fansho, da sauran haƙƙoƙin ma’aikatan gwamnati da suka yi ritaya, da kuma iyalan ma’aikatan da suka rasu a jihar.
Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al’adu na jihar, Malam Ahmed Maiyaƙi, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa, inda ya ce kudaden mutane 1,339 da suka cancanta a karkashin tsarin (CPS) ne Zasu amfana.
Ya ce, wannan sabon kaso ya kawo adadin kudaden fanshon da gwamnatin Uba Sani ta biya tun bayan hawanta mulki a watan Mayun 2023 zuwa Naira biliyan 21.455, wadanda suka mutane 9,683 suka amfana. A cewar kwamishinan, daga cikin wadanda za su amfana da sabon kudin, ‘yan fansho 210 na kananan hukumomi za su karbi Naira miliyan 515 karkashin tsarin DBS.
Ya kara da cewa Naira biliyan 3.144 kuma za a raba wa mutane 1,129 karkashin tsarin CPS, wadanda suka hada da ‘yan fansho 402 na ma’aikatan jihar da kuma 727 na kananan hukumomi. Ya ce, matakin na daga cikin kokarin gwamnatin jihar na magance basussukan fansho da kuma inganta tsarin biyan hakkokin ma’aikata bayan ritaya.
Kazalika, ya ce gwamnatin tana aiwatar da wasu sauye-sauyen harkokin kudaden gwamnati domin tabbatar da gaskiya, rikon amana da kuma dorewar tsarin fansho a jihar.
Kwamishinan ya bayyana cewa Gwamna Uba Sani ya yi imanin cewa biyan fansho ba alfarma ba ce, illa wajibi ne ga mutanen da suka sadaukar da shekarun rayuwarsu wajen yi wa jihar hidima.
Ya tabbatar da cewa gwamnatin za ta ci gaba da aiwatar da gyare-gyaren fansho tare da ƙoƙarin rage sauran basussukan da ake bin gwamnati, domin bai wa ma’aikata damar yin ritaya cikin mutunci da kwanciyar hankali.
