Isra’ila da Islamic Jihad sun yi wa juna ruwan makaman roka cikin dare

Sojojin Isra’ila da mayaƙan Islamic Jihad a yankin Gaza sun sake shafe tsawon dare suna kai wa juna hare-haren manyan makamai dai dai lokacin da alƙaluman Falasɗinawan da aka kashe cikin kwanaki 2 da faro rikicin ke tasamma 22.

Rikicin wanda ke matsayin mafi muni da aka gani tsakanin ɓangarorin biyu a watannin baya-bayan nan kowanne ɓangare na ci gaba da harba makaman roka ta yadda babu abin da ake jiyowa sai ƙarar harbawa da kuma tarwatsewarsu, kamar yadda majiyoyin labaran da ke sanya idanu kan rikicin ke bayyanawa a wani yanayi da Masar ke shige da fice don ganin ta sulhunta mayaƙan na zirin Gaza da Isra’ila.

Ƙungiyar Islamic Jihad ta bayyana kisan guda cikin kwamandojinta da ke jagorantar sashen harba makaman roka Ali Ghali wanda ta ce an kashe shi a zirin na Gaza tare da wasu mayaƙa.

Isra’ila ta sanar da cewa hare-harenta na baya-bayan nan ta kaisu ne kan sashen harba makaman rokan na Islamic Jihad wanda ya kashe tarin mutane, bayan da ministan tsaron Isra’ila Yoav Gallant ya bayyana cewa na harbo musu makaman fiye da 400 daga ranar Laraba zuwa jiya Alhamis.

A cewar ministan wannan mataki na Islamic Jihad da kuma varnar da hare-haren ke yi musamman a kudancin Isra’ila ya sanya su ci gaba da farmakar sashen harba makamai na ƙungiyar.