‘Yan Majalisar Dokokin Jihar Binuwai sun dakatar da zaman Majalisar saboda rashin biyansu ariyas na albashi da alawus-alawus na wata shida.
Dakatar da zaman ya sa wata dokotar fansho da Gwamnan jihar, Samuel Ortom, ya aika wa majalisar don neman amincewarta na fuskantar tsaiko.
Sabuwar dokar ta fansho na neman a riƙa bai wa tsofaffin gwamnonin jihar sabbin motoci guda huɗu duk shekara huɗu da kuma gida na din-din-din.
Kazalika, dokar na neman a bai wa tsaffin gwamnonin damar ɗaukar ma’aikata shida da kuma ma’aikata uku ga mataimakansu.
Hon. Bem Mngutyo ya faɗa a ranar Alhamis cewar, Majalisar “ta yanke shawarar ƙin zaman ne har sai an biya mu haƙƙoƙinmu.”
Ya ƙara da cewa, Gwamna mai barin gado ya gana da jigogin Jam’iyyar PDP a jihar a ƙarshen makon da ya gabata kan wannan batu.
A cewarsa, Gwamna Ortom ya yi alƙawarin zai biya su ariyas na albashi da alawus-alawus daga kason watan Mayu da jihar za ta karɓa daga Gwamnatin Tarayya kafin ya bar ofis nan da ‘yan kwanaki.