Ba ni ba sake fitowa takara bayan na kammala wa’adina na biyu, inji Gwamna Abdullahi Sule

Daga JOHN D. WADA a Lafiya

Gwamnan Jihar Nasarawa Injiniya Abdullahi Sule, ya ce da zarar ya kammala wa’adinsa na biyu a matsayin gwamnan jihar, ba zai sake fitowa takarar kujerar siyasa ba har ƙarshen rayuwarsa.

Gwamnan ya sanar da haka ne a lokacin da yake karɓar baƙuncin ‘ya’yan ƙungiyar masu aiko da rahoto wato Correspondents Chapel a turance na ƙasa reshen jihar ta Nasarawa waɗanda suka kai masa ziyarar taya shi murnar bikin ƙaramar Sallah da aka gudanar kwanan nan a gidansa dake garin Gudi dake yankin Ƙaramar Hukumar Akwanga a jihar.

Ya ce a yanzu Alhamdu lillah da yardar Allah kawo yanzu ya cimma burin rayuwarsa na kasancewa gwamnan jihar, inda ya samu damar bada nasa gagarumin gudunmawa wajen cigaba jihar a duka matakan rayuwa.

A cewar Gwamna Abdullahi Sule zuwansa karagar mulkin jihar ke da wuya sai ya tarar da ɗimbin ƙalubalai. Amma nan da nan sai ya yanke shawarar yin duka mai yuwa wajen tabbatar jihar ta cimma takwarorinta sauran jihohi a ƙasar nan musamman a fannin kasancewa xaya daga cikin jihohi da suka bunqasa a fannin ma’adanai musamman inda ake samar da man fetir da sauransu, inda a yanzu tuni aka gano rijiyar mai a jihar ta Nasarawa a ƙarƙashin shugabancinsa. Kuma a cewarsa a yanzu kwalliya ta biya kuɗin sabulu don ya cimma burin.

Ya ce: “Kuma ina so in yi amfani da damar nan in sanar da ku cewa ba ni ba sake fitowa takarar kowace kujerar siyasa a nan jihar da ma ƙasa baki ɗaya nan gaba bayan na kammala wa’adina karo na biyu a matsayin gwamnan jihar nan. Kuma na yanke shawarar ne don a yanzu kamar yadda kuka sani na cimma burina na bada gagarumar gudunmawa wajen cigaban jihar nan a duka matakai musamman fannin ma’adanai da albarkatun ƙasa da sauransu daidai da sauran jihohin ƙasar nan savanin yadda lamarin yake a da kafin in zama gwamna,” inji shi.

Daga nan sai gwamnan ya gode wa ƙungiyar ta masu aiko da rahotanni daga jihar dangane da ziyarar ƙaramar Sallar da suka kai masa, inda ya buqacesu su cigaba da gudanar da ayyukan su na yaɗa labarai yadda ya kamata inda ya tabbatar masu cewa gwamnatin a nata ɓangaren za ta cigaba da haɗa kai da su wajen cigaban jihar.

Tun farko da yake bayyana wa gwamnan maƙasudin ziyarar, shugaban ƙungiyar ta Correspondents Chapel a jihar Nasarawa Kwamared Isaac Ugboju ya ce sun kasance a gidan gwamnan ne don taya shi murnar bikin qaramar Sallar bana tare da taya shi murnar sake zaɓensa a matsayin gwamnan jihar karo na biyu.