Jam’iyyar NNPP na zargin Ganduje da sayar wa da ɗansa kadarorin gwamnati

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

Jam’iyyar NNPP a Kano, ta zargi gwamnatin APC ƙarƙashin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, da siyar da wasu kadarori mallakin gwamnatin jihar.

Zargin wanda ake kallon gwamnatin jihar na siyar da kadarorin ga ɗan gwamna ba bisa ƙa’ida ba, abin da Jam’iyyar NNPP ta ce ba za ta lamunta ba.

Har ma jami’iyyar ta ce za ta yi bincike da tabbatar da hukunci da zarar sun karɓi mulkin Kano a ranar 29 ga watan Mayu.

Jawabin hakan na zuwa ne ta bakin shugaban kwamitin karɓar mulkin jihar Kano na Jam’iyyar NNPP Abdullahi Baffa Bichi, yayin wata ziyara da ya kai Hukumar Kano State Public Procurement Bureau a yammacin ranar Laraba.

Zargin da ke nuna cewa hukumar na cikin kadarorin gwamnati da aka siyar wa da ɗan gwamna, akan kuɗi kimanin Naira miliyan 10, duk da cewa darajar hukumar ta kai miliyan 50, a cewarsa.

“Muna da labari gwamnati ta sayar wa da ɗan Ganduje kadarorin gwamnati sun fi ɗari duk mun sani, ba shi kaɗai ba ko wa aka sayar wa da kayan gwamnati sai mun bai wa gwamna mai shigowa shawara ta karɓe gurin saboda wuraren al’umma ne, don haka babu wani mahaluki da zai mallaka wa kansa,” a cewar Dr. Baffa Bichi.

Har ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto dai, gwamnatin Kano ba ta magantu akan zargin ba, amma mai magana da yawun Ganduje Auwalu Anwar ya shaida wa Freedom Radiyo cewa shi ba shi da masaniya akan wannan zargi.