EFCC ta kama tsohon ministan lantarki, Saleh Mamman kan zargin karkatar kuɗi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Jami’an hukumar yaƙi da cin hanci da hana yi wa tattalin arziƙin ƙasa ta’annati sun kama tsohon ministan lantarki na Nijeriya, Injiniya Saleh Mamman, wata majiya a ma’aikatar lantarki ta tarayya ta shaida wa BBC.

Kafofin yaɗa labaran ƙasar sun ce EFCC ta kama Saleh Mamman ne tun da sanyin safiyar Laraba inda suke ci gaba da tsare da shi a shalkwatar hukumar da ke Abuja.

Sun ce kamen na da alaƙa da zargin almundahanar wasu kuxaxie kimanin naira biliyan 22.

A cewarsu, jami’an Hukumar EFCC sun kama Saleh Mamman ne game da jerin bincike kan zargin aiwatar da wasu ayyukan lantarki.

Rahotanni sun ce ana zarginsa da haɗa baki da wasu jami’ai a ma’aikatar lantarki waɗanda ke kula da asusun ajiyar kuɗaɗen ayyuka a tashoshin lantarki na Mambilla da Zungeru, don karkatar da kuɗi Naira biliyan 22, tare da rabawa a tsakaninsu.

Kafofin yaɗa labaran sun ce bincike ya bankaɗo wasu kadarori a Nijeriya da ƙasashe waje masu alaƙa da jami’an da ake zargi, sannan an ba da rahoton gano miliyoyin nairori da daloli.