Tilas maniyyata su yi allurar Korona kwanaki 10 kafin a fara aikin Hajji — Saudiyya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ma’aikatar Hajji da Umrah ta ƙasar Saudiyya ta bayyana cewa ranar ƙarshe da maniyyata za su yi allurar rigakafin Korona ita ce kwanaki 10 kafin lokacin fara aikin Hajji.

Yin allurar rigakafin sharaɗi ne da zai ba su damar gudanar da aikin Hajji.

Hakan ya zo ne yayin da ma’aikatar ta amsa wa wani mutum tambaya a shafin ta na Tuwita.

Mutumin ya yi tambaya ko yin allurar Korona kashi na uku wani sharaɗi ne na yin aikin Hajji.

Ma’aikatar ta fayyace cewa kammala dukkan kashi na allurar rigakafin ya zama tilas wajen bayar da izinin aikin Hajji.

Ma’aikatar ta tabbatar da bayar da izinin aikin Hajji na 1444 a ranar 15 ga watan Shawwal, daidai da 5 ga watan Mayu.

Abin lura ne cewa ma’aikatar ta sanya ranar 10 ga watan Shawwal a matsayin ranar ƙarshe ga Mahajjatan cikin ƙasar da za su biya kaso na uku kuma na ƙarshe na kuɗin aikin Hajji.

Kashi na ƙarshe ya kai kashi 40 daga cikin kuɗin da aka ƙayyade da aka amince da su a lokacin wannan Hajji.