Ruwa da iska mai ƙarfi sun lalata gidaje a Damaturu

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN a Damaturu

Wani ruwan sama haɗe da iska mai ƙarfin gaske sun lalata wasu gidaje a garin Damaturu, hedikwatarta Jihar Yobe.

An shafe awa guda ana maka ruwan da iskan, tun gabanin Sallar La’asar a ranar Lahadi.

Da daddare bayan Sallar Isha, aka sake maka wani ruwan kamar da bakin ƙwarya na tsawon lokaci.

Akasarin gidajen da suka rushe suna unguwanni irin su Fawari na da Nainawa da gefen Rukunin Gidajen Ali Marami sai wani ɓangare na unguwar Pomfomari da makamantansu.

Wani magidanci da wannan iftila’in ya rutsa da gidansa a unguwar Nainawa, Malam Umar ya tabbatar da cewa, gidan nasa na laka ya rushe kuma a halin yanzu bai san inda zai sa kansa ba, don haka ya nemi mahukuntan jihar da su kawo musu ɗauki ko sa samu matsuguni.

Duk ƙoƙarin da Blueprint Manhaja ta yi don jin ta bakin Shugaban Hukumar Agajin Gaggawa ta jihar (SEMA) Alhaji Mohammed Goje kan ko suna sane da hakan, kuma wane ƙoƙari suke shirin yi don kai ɗauki ga waɗanda abin ya shafa, ya ci tura.