Barcelona ta sha kaye na uku a gasar LaLiga

Daga MAHADI M. MUHAMMAD

Barcelona ta sha kaye na uku a gasar LaLiga, bayan nasarar doke ta da ƙungiyar Rayo Vallecano ta yi da ƙwallaye 2-1.

Alvaro Garcia da Fran Garcia suka jefa ƙwallayen biyu a ragar Barcelona, kafin daga bisani Robert Lewandowski ya rama guda ɗaya.

Sai dai duk da rashin nasarar, Barcelona ta ci gaba da jagorancin LaLiga, abinda zai ba ta damar lashe kofin gasar na farko tun bayan kakar wasa ta 2018 da 2019.

A halin yanzu maki 11 a tsakanin Barcelona da babbar abokiyar hamayyarta Real Madrid, yayin da wasanni takwas suka rage wa kowannnensu a kakar wasa ta bana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *