Manyan sojojin Sudan sun amince da tsagaita wuta na sa’o’i 72

Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya, Antony Blinken, ya bayyana cewa, manyan sojojin Sudan sun amince da tsagaita wuta na kwana uku daga ranar Talata.

Blinken ya ce, “Biyo bayan tattauna mai zafi na sa’o’i 48, Rundunar Sojojin Sudan (SAF) da Rundunar RSF sun amince da matakin tsagaita wuta a faɗin ƙasar na sa’o’i 72 hours.”

Ya karatda cewa, “Amurka ta yi kira ga SAF da RSF da su tabbatar da tsagaita wutar nan take kamar yadda aka cimma.”

Haka nan, ya ce Amurka na aiki tare da abokan hulɗa don kafa kwamitin da zai tattauna batun tabbatar da tsagaita wuta na din-din-din a ƙasar ta Sudan.