Yau Shugaba Buhari zai tafi Ghana

A wannan Talatar ake sa ran Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, zai ziyarci ƙasar Ghana don halartar taron ƙolin shugabannin ƙasashen yankin tekun Guinea da za a gudanar a Accra, babban birnin ƙasar.

Hakan na ƙunshe ne ciki wata sanarwar da Fadar Shugaban Ƙasa ta wallafa a shafinta na Tiwita a ranar Litinin.

Sanarwar ta ce, ta ce shugaban zai bar Nijeriya ranar Talata, 25 ga Afrilu domin halartar taron, wanda Shugaban Ƙasar Ghana, Nana Akuffo-Ado, zai jagoranta.

Ana sa ran shugaban zai gabatar da jawabi a taron wanda zai tattauna dabarun ƙarfafa zaman lafiya da tsaro da yaƙi da masu aikata miyagun laifuka a gaɓar tekun yankunan ƙasashen.

Buhari zai tafi taron ne bisa Yayin halartar taron ne bisa rakiyar Ministan Harkokin Ƙasashen Waje, Geoffrey Onyeama, mai bai wa Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Babagana Monguno (mai ritaya), Daraktan Hukumar Tattara Bayanan Sirri, Ambasada Ahmed Rufai Abubakar da sauransu