Donald Trump ya gurfana gaban kotu, ya musanta zargin da ake yi masa

Tsohon Shugaban Ƙasar Amurka, Donald Trump, ya musanta zarge-zargen laifuka 34 da ake tuhumar sa da aikatawa, bayan wani bincike da ya gano cewa ya bai wa wata jarumar fina-finan batsa mai suna Stormy Daniels, toshiyar baki.

Trump wanda ya miƙa kansa ga Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Amurka da ke Manhattan, shi ne Shugaban Ƙasar na farko da ya fara fuskantar tuhuma da ta danganci aikata manyan laifuka.

Rahotanni na nuni da cewa, Trump ya ba wa jarumar fina-finan batsar kuɗin toshiyar bakin ne a shekarar 2016.

Bayan da ya bayyana gaban kotu, tsohon shugaban na Amurka ya wallafa saƙon da yake yi wa mahukuntan ƙasar izgilanci, yana mai cewa da alama suna ƙoƙarin tsare shi ne.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *