Ta leƙo ta koma wa Haruna Sani na hukumar NASENI

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya umarci Mataimakin Shugaban cibiyar NASENI, Farfesa Mohammed Sani Haruna, da ya gaggauta barin ofishinsa.

Sanarwar da ta fito ta hannu Daraktan Yaɗa Labarai na Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya, Mr Willie Bassey, ta ce Buhari ya bai wa Sani Haruna umarnin ya miƙa ragamar aiki ga jami’i mafi girman muƙami a cibiyar.

“Wannan ya biyo bayan janye tsawaita wa’adin zama a ofis da Buharin ya yi a ranar 2 ga Afrilun 2023 zuwa 2 ga Afrilun 2025 duba da Haruna Sani ya kammala wa’adinsa na shekara biyar riƙe da cibiyar.

“Buhari ya yaba wa Farfesa Haruna dangane da nasarorin da ya samu a fannin injiniya wanda ɓangare ne na tattalin arzikin ƙasa.

“Kana ya yi masa fatan alheri a harkokinsa da zai saka a gaba,” in ji sanarwar.